Kayan hadi
- Doya
- Attarugu
- Albasa
- Kwai
- Magi
- Gishiri
- Kori
- Mai
Yadda ake hadawa
- A fere doya a yanka ta sai a wanke a sa a tukunya a dora a wuta da dan gishiri.
- Idan ya nuna sai a sauke a kawo turmi mai tsafta a daka doyar sama-sama.
- Sai a dauko jajjagen attarugu, albasa, sunadarin dandano da kori a zuba a kan doyar a juya su hadu sosai.
- Daga nan sai a rika dunkula doyar a yi ta kamar kwallo.
- Sai a fasa kwai a dora kasko a wuta a sa mai.
- Idan man ya yi zafi sai a rika dauko kwallon doyar ana tsomawa a kwai ana soyawa a man.
- Idan ya yi sai a kwashe.
Shi ke nan sai ci.