Zogale abinci ne mai matukar amfani a jiki, wanda ake sarraffa shi ta hanyoyi daban-daban kamar kwado, miya, magani da dai sauransu.
Shi ya sa a wannan karon muka yi wa uwar gida tsarabar yadda ake yin miyar zogale, wadda ana iya cin ta da sakwaro ko tuwo.
Kayan miya
- Zogale
- Nama
- Sunadarin dandano
- Albasa
- Gyada
- Citta
- Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
Da farko za a wanke naman a sa albasa da sunadarin dandano a dora a wuta ya tafasa sosai.
Sai a gyara zogalen a ajiye a gefe, a jajjege attarugu da alabasa da tafarnuwa da citta a ajiye a gefe.
Idan naman da ya yi sai a zuba jajjaggen attarugun a tsayar da ruwan miya.
Daga nan sai a sanya gishiri da sinadarin dandano a rufe ya yi kamar minti biyar.
Idan ya yi sai a zuba zogale a rufe, shi ma ya samu kamar minti biyar.
Bayan nan sai a zuba gyada a rufe, idan ya nuna sai ki sauke.
Dabarun girki
Ga wasu dabarun girki da uwar gida za ta iya amfani da su:
- Kafin a bare bayan albasa a saka ta a cikin firinji ta yi sanyi, hakan zai hana ta yi yaji idan nan yankawa.
- Bayan a fere dankali a sa a cikin ruwan sanyi domin kar ya sauka launi