✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake fanken ayaba

Yadda ake fanken ayaba (Banana balls)

Jama’a Assalamu Alaikum, yaya azumi. Yau kuma mun kawo muku yadda ake yin fanken ayaba, wato Banana balls a Turance.

Amma kafin mu shiga ka’in da na’in, ga abubuwan hadin da ake bukata:

– Ayaba

– Fulawa

– Kwai

– Madara

– Sukari

– Baking powder

– Yis

– Ruwa

– Man gyada

Yadda ake hadawa

– A tankade fulawa da baking powder a cikin kwano mai zurfi, a zuba madara da sukari sannan a fasa kwai a ciki

– A yayyanka ayaba kanana a zuba a ciki sannan a kwaba sai ya hadu sosai

– Sai a zuba yis da ruwa, a sake kwabawa sosai har sai ya yi kauri kamar kullun fanke

– A rufe kamar na minti 30 ko fiye da haka

– Sai a dora tukunya a wuta a zuba man gyada

– Idan man ya yi zafi sosai sai a rika jefa kullin a ciki ana soyawa kamar fanke

– Idan ya soyu sosai sai a kwashe

– A barbada sukari a kan soyayyen fanken

Ana iya ci da shayi ko da duk wani lemon sha.