Jama’a barkanmu da warhaka. Yau kuma ga mu dauke da yadda ake girka alalan gurjiya.
Kayan hadi
– Gurjiya
– Manja
– Tattasai
– Albasa
– Gishiri
– Attarugu
– Sinadarin dandano
– Garin curry
– Ledar santana
– Ruwa
Yadda ake hadawa
– Za a nika gurjiya ta yi laushi sosai sai a tankade da abun tata a cire tsakin.
– A zuba manja a cikin tankadadden garin sai a kwaba da hannu sannan a zuba tafasasshen ruwa ba mai yawa ba, a kwaba sosai da ludayi.
– Sai a zuba markadadden tatasai, albasa, da attarugu da kuma kori da gishiri da kayan dandano.
– A zuba ruwa har sai kaurin kullun ya yi daidai yadda ake so.
– A zuba hadin a leda sai a kulla yadda ake so.
– Sai a dora a tukunya da ruwa a wuta, idan ruwa ya tafasa sai a zuba kullin hadin a ciki a bari har sai ya nuna.
– Idan alalen ya nuna sai a saukar daga wuta.
Shi ke nan sai ci!