Barkanmu da warhaka uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya.
A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa domin yi wa Manyan Gobe a matsayin abin karyawa a duk safiya ko kuma yin sa domin sha’awar cinsa ko kai wa aminan arziki.
- AFCON2021: Senegal da Masar [Final]
- Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindigar da suka kai hari kauyen Zamfara
Kamar yadda muka yi muku alkawari za mu ci gaba da kawo muku nau’o’in girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
- Fulawa
- Kwai
- Sukari
- ‘Baking powder’
- Ayaba
- Madara
- Bata
Yadda ake yin hadin:
A samu ayaba biyu a kwaba su da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da sukari da madara, sannan a kwaba.
Bayan haka a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sai a fasa kwai biyu da kwababbiyar ayabar a cikin fulawar da aka yi mata hadin sukari da sauransu.
Sai a gauraya su sosai su kwabu. Sannan a dauko tukunyar gasa burodi a zuba sannan a sa a gidan gasa burodi. Bayan minti 45 sai a cire.
Za a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandani sabon salon burodi.