Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta yi Allah wadai da masu amfani da miyagun kwayoyi, musamman tabar wiwi a cikin girke-girkensu.
Shugaban NDLEA na kasa, Birgediya-Janar Buba Marwa (mai murabus) ne ya bayyana takaicin yayin da yake jawabi a wajen wata lacca ranar Alhamis a Legas.
Ya ce, “Mutane na amfani da miyagun kwayoyi wajen girka abinci da farfesu da sauransu, hakan na da hadari kuma abin a yi tir da shi ne.”
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito taron laccar ya maida hankali ne wajen tattauna batun da ya shafi ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasan Afirka.
Haka kuma, laccar ta tabo illar da ta’ammali da miyagun kwayoyi ka iya yi ga tattalin arzikin Najeriya da Zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban hukumar ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya duk da kokarin da NDLEA ke yi wajen yaki da matsalar.
Buba Marwa ya jaddada cewa, “Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu sarrafa kwayoyin da ma masu safararsu a kasar nan.”
(NAN)