Barkanmu da sake haduwa da ke uwargida a wannan filin namu na girke-girke. Kamar yadda Hausawa ke cewa duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Wannan dalili ya sa muka koma gargajiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar taushe da burabusko da man shanu. Tare da fatar za a gwada yi wa maigida. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da ake bukata
- Garin burabusko
- Alayyahu
- Nikakkiyar gyada
- Magi
- Kori
- Garin tafarnuwa
- Man shanu
- Tattakwashi
- Manja
- Attarugu
- Albasa/ Tumatir
Hadi
A dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai a rage wutar sannan a zuba garin burabusko ana gaurayawa sannan a rufe. A sake rage wutar a jira kamar na tsawon minti ashirin. Sai a kwashe da mara a sa a kwano a ajiye a gefe.
A silala nama da tattakwashi da albasa da gishiri kadan. Bayan haka, sai a jajjaga tumatir da attarugu. A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja idan ya yi zafi sai a zuba albasa idan albasar ta soyu sai a zuba jajjagaggen kayan miyan. A yi ta juya su har sai sun soyu.
A dauko nikakkiyar gyada a dama sannan a zuba wannan romon nama da silalen tattakwashi a cikin kayan miyar. Bayan haka, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa sai a gauraya. Idan suka tafasa, sai a zuba kwababben gyadar nan a cikin hadin kayan miya a sake gaurayawa.
A yayyanka alayyahu sannan a wanke da ruwan gishiri domin wanke datti da cututtukan da ke cikin ganyen. Sai a wanke sau uku, a sake juya miyar. A jira gyadar ta nuna sosai sai a zuba wankakken alayyahu sannan a rufe.
Bayan minti biyar, sai a sake gauraya miyar. Sannan a sauke a dauko man shanu a soya da albasa sai a zuba a kan miyar. Girki ya nuna! A dauko tuwon burabuskon nan a zuba masa miyar a kai. A bai wa maigida. A ci dadi lafiya!