✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ake Shinkafar Lambu Da Miyar Kaza

Kayan lambu na taimaka wa garkuwar jiki yaki da cututtuka, da rage hadarin kamuwa da cututtukan siga, zuciya, da ciwon gabobi.

Peas da karas da koren wake duk kayan lambu ne da ke taimaka wa garkuwar jikin dan Adam yaki da cututtuka, da rage hadarin kamuwa da cututtukan siga, zuciya, da ciwon gabobi.

Kaza ma a hannu guda na kara jini da narka kitsen nan mai wuyar narkewa a jikin dan Adam da sauransu.

Yau a filin namu, mun kawo muku yadda ake yin shinkafar lambu da miyar kaza:

Abubuwan da ake bukata

  • Shinkafa
  • Karas
  • Koren wake
  • ‘Peas’

Hadi 

  1. A dafa shinkafar a yi mata tafasar farko sai a wanke a tsame ta.
  2. Sai a kankare karas a yayyanka shi kanana.
  3. A wanke koren wake a yayyanka kanana a sake ajiyewa a gefe.
  4. A wanke peas shi ma a wanke.
  5. A sake zuba wani ruwan zafi a wuta, bayan ya tafasa, sai a zuba shinkafar da yankakken karas da koren wake da peas su dahu tare.
  6. A wanke kaza sai a tafasa da albasa da gishiri da thyme.
  7. Idan ta yi laushi, sai a fara soya albasa, sannan tumatir, da attaruhu.
  8. Da zarar sun soyu, sai a zuba sinadarin girki, da kori, da tafarnuwa.
  9. A dauko wannan sulalen naman kazan a zuba da dan romo kadan.
  10. Za a iya hada wannan girkin da sauce din kaza ko na koda, sai ci.