✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake miyar yalo

Yadda ake hada miyar yalo da kuma abin da ake ci da shi

Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke, inda a yau za mu kawo yadda ake yin miyar yalo.

Kayan hadi

  • Yalo
  • Bandar kifi
  • Kanapari
  • Tumatir
  • Tatashe
  • Attarugu
  • Albasa
  • Gishiri
  • Ganyen kori
  • Sinadarin dandano
  • Man ja

Yadda ake hadi

1. A wanke yalo a yayyanka.
2. Sai a dora tukunya a wuta a zuba ruwa da yalon a dafa.
3. A markada dafaffafen yalon da tatasai da attarugu da tumatir, albasa da kananfari
4. Dora tukunya a wuta da manja sai a zuba bandar kifi a soya sosai
5. A dauko markaden da aka yi sai a zuba a ci gaba da juyawa.
6. A zuba gishiri, magi da kori a gauraya.
7. A rage wuta sannan a rufe na tsawon minti uku.
8. Sake budewa a juya har sai ta nuna.
9. A sauke, sannan a barbadda ganyen kori sai a juya.
Ana iya ci da dafaffiyar doya.