Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan fili namu na girke-girke. Kamar yadda na saba fadi cewa yana da kyau idan yau an taba miyar birni, gobe kuma sai a sharbi miyar kauye.
Zogale na dauke da sinadaran da suke maganin cututtuka da dama, don haka yana da kyau a koyi yadda ake girka wannan miya.
Akwai hanyoyi da dama da ake girka wannan miya. A yau na kawo muku irin nawa salon girka miyar zogale walau danye ko busasshe.
Za a iya cin wannan miya da tuwon shinkafa ko na dawa da masara da kuma na alkama. Abubuwan da za a bukata:
- Busasshen zogale
- Attarugu
- Nikakkiyar gyada
- Tumatir
- Albasa
- Wake
- Sunadarin Dandano
- Garin tafarnuwa
- Manja
- Nama
- Wake
Yadda ake yin hadin:
Da farko dai za a yanka albasa sannan a jajjaga tumatir da attarugu. A dafa wake ya nuna sosai sannan a ajiye a gefe.
A silala nama da gishiri da albasa. Bayan haka, sai a dora tukunya a wuta sannan a zuba manja, sai a soya albasa ta dan fara soyuwa sannan a zuba jajjagen kayan miyar.
A yi ta soyawa har sai ta soyu kamar miyar dage-dage. Sannan a dauko wannan romon silalen nama da naman a zuba.
A zuba magi da garin tafarnuwa da kori. Sai a rufe tukunyar, bayan ta tafasa sannan a zuba wannan waken a ciki a gauraya har sai ta gaurayu.
Sannan a dauko nikakkiyar gyadar nan a zuba ruwa a gauraya kamar za a yi kunu sannan a zuba a gauraya.
Bayan gyadar ta nuna, sai a dauko busasshe ko danyen zogalen a zuba a gauraya sannan a rufe.
Haka za a yi ta yi har sai zogalen ya nuna sannan a sauke.