Dashishi abincin gargajiya ne da ke kara lafiya, kuzari, da kuma gina jiki.
A yau shi ne abin da muka yiwo muku tsarabar yadda ake girkawa.
Kayan da ake bukata:
- Alkama kofi 8
- Mai kofi 1
- Gishiri kadan
- Ruwa
Yadda ake yi:
- Ki sami alkama ki tsince ta sai a surfeta a cire dusar.
- A wanke ta, a bari ta bushe, sai a nika a barzo ta amma kada ta yi gari sosai.
- A zuba ruwa a tsame ta yadda barjin zai yi laushi idan an turara shi, sai a tsame.
- A sami madanbaci a turara shi, har sai ya fara cuccurewa,
- Daga nan sai a zuba mai da gishiri a juya sosai amma a sauke.
- Sai a sa mai yadda zai warware, a kara mayarwa shi kan wuta.
- Idan ya yi za a ji yana kamshi, sai ci.
Ana ci da miyar taushe ko miyar ganye ko duk miyar da ake so.