Assalamu alaikum uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya azumi?
Yau na kawo muku yadda ake miyar nikakken nama.
Wajibi ne ga uwargida ta koyi girki iri-iri domin samar wa ’ya’yanta ingantaccen abincin da za su kara musu sinadarai a jikinsu da kuma burge maigida.
Ina kira ga mata da su dage su koyi nau’ukan girki domin akan gaji da cin abinci iri daya.
Kayan hadi
- Nama
- Tumatir
- Albasa
- Attaruhu
- Man gyada
- Tafarnuwa
- Citta
- Sinadarin dandano
- Kori
Yadda ake yin hadin
- A samu jan nama wanda babu kitse a cikinsa, a markada shi a ajiye a gefe.
- Sai a yayyanka albasa da tumatir sannan a jajjaga da attaruhu da tafarnuwa.
- ِA dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan a ciki.
- A sa albasa da tumatir da garin citta kadan da jajjagen attaruhu da tafarnuwa a yi ta soyawa.
- A dauko nikakken naman a zuba a ci gaba da juyawa.
- Sai a zuba magi da kori a gauraya.
- A rage wuta sannan a rufe na tsawon minti biyu.
- Aai a sake budewa a juya har sai ta nuna sannan a sauke.
Za a iya cin wannan miyar da dafaffiyar doya ko farar shinkafa ko wani abin da ake sha’wa.
A ci dadi lafiya.