✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kunun ridi, dabino da kwakwa

Zai yi dadi sosai idan aka yi bude-baki da shi da azumi

Assalamu Alaikum, barkanmu da warhaka. Yau muna dauke ne da yadda ake hada kunun ridi, dabino da kwakwa a filinmu na grike-girken azumi.

Kayan hadi

– Ridi

– Dabino

– Kwakwa

– Garin madara

– Sukari

– Fulebo

Yadda ake hadawa

– A surfa ridi a wanke, a cire dusar.

– A yayyanka kwakwa kanana a ajiye a jefe.

– A jika dabino har sai ya yi laushi, sai a cire kwallayen.

– A zuba ridin da yankakken kwakwa da dabino da ruwa kadan a blender a markada sosai.

– A tace sai a zuba madara, sukari da flavour.

– A zuba a mazubin ruwa a saka a firinji har sai ya yi sanyi sosai.

Shi ke nan, a sha dadi lafiya!