✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu nemi taimakon Allah a kwanakin ƙarshe na Ramadan

Lallai mu yi ta addu’a mu roƙi Allah da kyawawan sunayenSa Ya kawo mana karshen wannan masifa da tashin hankali.

Masu magana kan ce komai ya yi farko zai yi karshe, ban da ikon Allah, shi ba ya da farko kuma ba ya da karshe.

Allah Shi ne Ya halicci komai Ya sa masa farko da karshe amma ban da ikonSa.

Kamar yadda muke ta lissafi da dokin zuwan wannan wata mai dimbin falala da alherai, yau ga shi muna shirin ban-kwana da wannan babban bako abin karramawa.

Watan Azumin Ramadan yana daga cikin watannin shekara da ake soma yi musu tanadi tun kafin zuwansu.

Za a yi ta shiri na ciye-ciye da dafe-dafe da ibada da karatun Alkur’ani da Sallar dare da kyauta da sadaka da taimako da sauran ayyukan ibada don neman yardar Allah Madaukaki, muna addu’a kuma muna rokonSa Ya karbi ibadunmu Ya sa muna cikin bayinSa wadanda suka rabauta a cikin wannan wata.

Wasu daga cikin mutanen jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sakkwato na daga cikin mutanen da suka ga watan azumin nan a mawuyacin hali.

Domin dukkan tashe-tashen hankalin da jihohin suke fama da su lokaci mai tsawo, gabatowar wannan wata na falala da bayi kan shagala da neman gafara da yardar Allah, su wadancan ’yan bindiga da ke jihohin Allah bai kaddara su saduda su bi Allah da AnnabinSa a wannan wata ba.

Duk da irin yadda bayi kan bar ayyukan assha su shagala da neman gafarar Allah, su ko a jikinsu, suna ci gaba da bakanta rayuwar bayin Allah da suke azumi, suna ci gaba da cin zarafin bayin Allah suna keta musu haddi.

Tashin hankali da firgici da suka jefa dubban iyalai a wadannan yankuna a wannan lokaci da Musulmi suka shagala da ibada da bauta ga Mahalicci ba a cewa komai.

Su sun shagala da sacewa da kashewa da karbe wa mutane dukiyarsu da sunan fansar ’yan uwa da danginsu da aka sace.

Mutanen kauyukan Jihar Zamfara ba su yi wa kowa laifi ba, su ma ’yan kasa ne kamar kowa, sun cancanci kariya daga hukumomi kamar yadda kowa ke bukata, amma hukumomi sun gaza kare rayukansu da dukiyoyinsu, sun zama kamar wasu daban da sauran al’ummomin wannan kasa.

Ana shiga kauyukansu a kwashe musu dukiya a kwace musu amfanin gona.

Dan abin da suka mallaka duk sun sayar sun tura wa wasu lalatattun mutane a daji, hukumomi suna kallo sun gaza sauke nauyin da Allah Ya dora musu.

Kamar yadda koyaushe muke nanatawa, wannan tashin hankali da ake fama da shi a Arewa maso Yamma, matukar ba a tashi tsaye an yake shi ba, to, muna cikin tsaka-mai-wuya.

Domin kuwa al’ummomin da ake kora daga garuruwansu da gidajensu da gonakinsu da dabbobinsu, babbar barazanar da ke cikin wannan shi ne hakan zai haifar da rashin abinci ga al’umma, domin mutanen kauyukan da ba su san komai ba sai noma da kiwo, yau an wayi gari sun koma mabarata, saboda wasu lalatattu da suka dauki makamai suka hana su zaman lafiya.

Hukuma kuma da yake wajibinta ne ta samar musu da tsaron rayuka da dukiyoyi, kullum zance daya take yi, shi ne cewa ana daukar mataki, duk da a zahiri bama iya ganin alfanun matakin da ya dace, amma mutane ba su fita daga cikin wannan mawuyacin hali da wahala ba. Masu iya magana sun ce idan aka bi ta barawo, a bi ta mabi sawu.

Dukkan wadannan abubuwa da suke faruwa, bayanai sun nuna cewa da dan gari akan ci gari.

Ana samun bayanan da suke nuna cewa akwai hadin baki tsakanin ’yan uwa da dangin al’ummun wadannan yankuna da suke fama da tashin hankali da wadannan ’yan bindiga.

Bayanai da rahotanni sun sha nuna cewa an ga inda ’ya’ya suke hada kai da ’yan bindiga a sace mahaifinsu, ko a ji an ce mace ta hada kai da ’yan bindiga an sace mijinta domin a karbi kudi a hannunsa ko surukai su hada kai da ’yan bindiga domin a karɓi kuɗi a hannun surukinsu koma uba ya hada kai a sace dansa.

Wannan wacce irin masifa ce? Saboda haka, ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga al’umma su yi amfani da wannan dama ta ƙarshe da suka samu na kwanakin ƙarshen watan Ramadan domin neman yardar Allah, mu kuma nemi Allah Ya kawo mana ƙarshen wadannan fitinu da suka dame mu.

Waɗannan ’yan bindgia ’yan uwanmu ne da muke rayuwa tare da su, suna magana da yare irin namu, suna sanya tufafi irin namu suna rayuwa irin tamu, amma su sun ratse hanya, sun dauki makamai babu gaira babu dalili suna cutar da ’yan uwansu.

Lallai mu yi ta addu’a mu roƙi Allah da kyawawan sunayenSa Ya kawo mana karshen wannan masifa da tashin hankali, ko ma samu mutane su koma garuruwansu su ci gaba da rayuwa kamar kowa, su yi noma da kiwo domin samun abinci da kuma rufa wa kansu asiri. Lallai ana jiye mana tsoron fadawa halin yunwa da fatara a nan gaba.

Domin idan mutane suka bar gonakinsu ba su yi noma ba saboda tashin hankali, zai zama noman da za a yi kadan ne a kan wanda ya kamata a yi, kuma kadan din da aka noma, zai yi matukar tsada ta yadda abinci zai gagari masu karamin karfi.

Ba ma fatan mu kai ga irin wannan hali, amma lallai ne mu tashi tsaye mu nemi hukumomi a kan su yi duk mai yiwuwa wajen ganin al’ummarsu ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan shi ne zai sa rayuwa ta dore a samu kwanciyar hankali da karuwar arziki.

Malamai sun sha gaya mana irin mummunan tanadin da Allah Ya yi wa masu kisan kai bisa ganganci, kisan irin na zalunci da cin zali da nuna fin karfi.

Lallai an tsoratar da mutane a kan daukar makamai su fuskanci al’umma saboda zalunci da rashin tsoron Allah.

Haka kuma, a cikin wannan wata na Ramadan mai dimbin falala, malamai sun gaya mana cewa kwanaki goman karshe na watan sun fi sauran kwanaki falala a cikin watan, domin a cikinsu ne ake samun dacewa da daren Lailatul Kadari, wanda alheran da suke cikinsa sun shafe na wata dubu.

Don haka, ko da mun yi sake a farkon watan, to mu yi kokari a ’yan kwanakin da suka rage, mu nemi gafara da yardar Allah.

Mu roki Allah Ya gafarta mana laifuffukanmu, Ya amintar da mu a garuruwanmu da kauyukanmu da gidajenmu, Allah Ya kawo mana dawwamammen zaman lafiya.

Wadannan mutane da suka dauki makamai suke kisa babu gaira babu dalili, suke sace mutane suna karbar makudan kudi a hannun danginsu, mu yi addu’ar Allah Ya shirye su, idan kuma ba masu shiryuwa ba ne Allah Ya yi mana maganinsu, Allah Ya ba mu natsuwa da kwanciyar hankali a gidaje da unguwanni da garuruwa da jihohinmu da kasarmu baki daya.

Shugabanni kuma yana da kyau su ji tsoron Allah su yi abinda ya dace domin kawar wa wannan al’umma damuwar da take hana su sukuni.

Su ma shugabannin suna bukatar al’umma su taya su da addu’a a kan Allah Ya ba su mashawarta nagari, wadanda za su taimaka musu wajen share wa al’umma hawayensu, amin.

Muna fata za mu ga karshen azumin nan lami lafiya, Allah Ya karbi ibadunmu Ya sa muna cikin bayinSa wadanda suka samu rabauta a wannan wata.

Da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya.