✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada ruwan gishiri da sukari

Shan ruwan gishiri da sukari shi ne taimakon farko da za a ba mai amai da gudawa.

Saboda yawan samun rahotannin bullar cutar amai da gudawa a kasar nan a ’yan kwanakin nan, za mu duba yadda ake hada ruwan gishiri da sukari.

Shan ruwan gishiri da sukari shi ne ginshikin taimakon farko da za a ba wa mai amai da gudawa, don gudun galabaita da salwantar rai musamman ma yara.

Shi ruwan gishiri iri-iri ne?

Akwai wanda ake hadawa a gida akwai na Hukumar Lafiya ta Duniya da ke zuwa a sacet mai suna WHO ORS ko UNICEF ORS.

Akwai na asibiti da ake sawa ta jijiya.

Dukkansu ana ba mai gudawa da ruwan jikinsa ya yi karanci, musamman yara wadanda gudawa ko zawo ya fi galabaitarwa.

Ana gane cewa ruwan jikin yaro mai gudawa ya fara karanci ta alamomi kamar haka;

1. Yaushin fata,

2. Kuka ba hawaye,

3. Bushewar lebba,

4. Rashin kuzari,

5. Ko idanuwa su fada

6. Sauyawar launin fitsari ko yana yi kadan, ko wanda launinsa ya yi duhu, ko ruwan dorawa sosai.

Da zarar an ga koda daya daga wadannan alamu, sai a fara ba da ruwan gishiri da sukari wanda ake hadawa a gida, kafin a tafi asibiti.

Ana hada irin wannan ruwa ne idan aka zuba gishiri kamar karamin cokali daya da sukari karamin cokali goma a matsakaicin kofi biyu na ruwa (wato a iya sa rabin karamin cokalin gishiri da karamin cokali biyar ke nan a kofi guda).

Ko a sayo na hukumar lafiya dan sacet a zuba daidai yadda aka rubuta a takardar.

Sai a gauraya a rika bayarwa a hankali, ba lokaci guda ba.

Duk a wannan hali ana ba marar lafiyar abinci ya ci kamar yadda ya saba ko da gudawa ba ta tsaya ba.

Idan yaro ne wanda ba a yaye ba, shi ma za a ci gaba da shayar da shi.

Idan ba amai sosai kuma yana karba nan da nan za a ga ya farfado, amma idan yana amayarwa, dole a tafi asibiti mafi kusa.

Ba lallai sai irin wannan ruwan gishiri da sukari na hadi ba, akan iya ba da ruwan da aka fara dafa shinkafa da shi, wato ruwan da ke bararraka shinkafa idan ta dauko dahuwa, don shi ma ruwan yana da gishiri da sukari (gishirin da aka barbada, shi kuma sitacin shinkafar sukari ne).

Haka ma farfesu marar yaji ko romo, shi ma a iya ba mai gudawa don ya mai da ruwan jikinsa.

Su wadannan ruwan shinkafa da na romo bincike ya nuna bayan karin ruwa da sinadaran jini a jiki, har sukan taimaka wajen tsayar da zawo.

Wadannan su ne ruwan gishiri da sukari na gida.

Kai har lemon kwalba a irin wannan yanayi ba laifi a ba mutum ko yaro in dai yana karba.