✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada jus din kankana

Assalamu alaikum jama’a, a yau na zo muku da yadda ake hada jus din kankana. Za a iya yin shi domin sayarwa ko kuma domin…

Assalamu alaikum jama’a, a yau na zo muku da yadda ake hada jus din kankana.

Za a iya yin shi domin sayarwa ko kuma domin sha a gida ko biki.

  • Kayan hadi
  • Kankana
  • Sukari
  • Madara
  • Flavor

Yadda ake hadawa
A yanka kankanar a zuba ta a blender a markada ta sosai ta yi sumul babu sauran gudajin kankana.

A tace markadaddiyar kanakar sosai sannan a zuba sukari daidai bukata a ciki.

Daga nan sai a zuba madarar ruwa da flavor cikin chokali a cikin kankanar da aka tace sannan a jujjuya.

Idan an gama sai a sa a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a sa kankara a ciki gwargwadon yadda ake so a sha.

Yadda ake hadda ‘kankana jus’ cikin sauki ke nan, da fatar za’a jarraba.