Juice din Beetroot yana da amfani ga dan a matsayin kayan marmari.
Beetroot na rage alamar tsufa, gyara fata, wanke ciki da jini, kara lafiyar hanta, rage hawan jini da kuma kara tsawon gashi. Yana kuma kara kuzari, kare zuciya, rage hadarin kamuwa da cutar kansa da kuma matsalar kwakwalwa.
Ga yadda ake yin sa:
Kayan hadi
- Beetroot
- Citta
- Lemo
- Na’ana’a
- Lemon tsami
Yadda ake hadin
1. A wanke beetroot, chita, na’ana’a, Lemo da lemo tsami da gishiri.
2. Sai a dauraye su sosai sannan a yayyanka su kanana.
3. A markada beetroot, Citta, na’ana’a da lemon tare.
4. A tace markaden a zubar da tsakin.
5. A matse ruwar lemon tsami sai a sa a ciki.
6. A ajiye hadin a firinji ya yi sanyi
6. Beetroot ‘juice’ ya fi kyau idan aka zuba a kofin gilashi tare da kankara, sai sha.