Assalamu alaikuma jama’a, yau na kawo muku yadda ake hada Fruity Zobo. Hadin Zobo ne na musamman da za a iya yi domin sha a gida ko taro ko kuma sayarwa. Ga yadda ake hadawa:
Abubuwan da ake bukata
- Zobo
- Sukari
- Abarba
- Lemo
- Gurji (cucumber)
- Karas
- Citta
- Kanumfari
- Flavor
Yadda ake hadawa
A dora ruwa daidai bukata a tukunya ya tafasa, sannan a saka bawon abarba a ciki.
Sai a dauko gyararren citta da kanunfari a zuba a ciki daidai bukata.
Daga nan sai a sa yankakken gurji da lemo a ciki a bari ya yi ta tafasa na minti 15 zuwa 20.
Bayan nan sai a zuba zobon a ciki tafashehen ruwan a bar shi na tawon minti 15 kafin a sauke.
Idan ya huce sai a dauko ruwan nikakakken karas da abarba da gurji da aka riga aka tace a sanya a ciki.
A tabbata sun niku sosai an kuma tace da kyau. Za kuma a iya yin su daban-daban ko a hade.
Daga nan sai a sanya flavor cikin chokali da sukari juya sosai.
Za a iya sanya inabi ko yankaken gurji a ciki in ana bukata.
Sai a je a saka a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a saya kankara a ciki – gwargwadon bukata.
Wannan shi ne yadda ake hada Fruity Zobo.
A sha Fruity Zobo lafiya.