Assalamu alaikum uwargida yaya yara? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya.
Idan aka ambaci kalmar ‘fate’ nau’o’in fate da dama zai zo a tunaninmu. Akwai fate da dama da ake yi kamar: faten doya da faten wake da faten tsaki da sauransu.
A yau za mu shiga gargajiya ce don haka za mu koya muku yadda ake faten tsaki da gyada. A sha fate lafiya.
Abubuwan da ake buqata
- Tsaki
- Kifi banda
- Attarugu
- Albasa
- Tumatir
- Alayyaho
- Nikakkiyar gyada
- Magi
- Kori
- Garin tafarnuwa
- Garin citta
- Manja ko man gyada
Yadda ake yin hadin
Da farko za a wanke tsakin masara ya zamo babu tsakuwa ko kadan sannan a dora tukunya a wuta a zuba manja ko man gyada sannan a yayyanka albasa a zuba da nikakken kayan miya a soya tare da bandar kifin.
A zuba magi da kori da garin tafarnuwa da na citta sannan a kwaba gyada kadan a zuba ta yi ta tafasa sannan a zuba tsaki har sai ya nuna.
A zuba tsakin kadan domin yana kumbura. Idan tsakin ya nuna sai a zuba yankakken alayyahon da aka riga aka wanke da ruwan gishiri kuma aka yayyanka.
Sannan sai a rage wutar risho. Bayan minti uku sai a sake gaurayawa a sauke.
A sha fate lafiya.