✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dambun kifi

Yadda ake dambun kifi

Shin kun san yadda ake girka Dambun Kifi? Ku biyo mu yau ku sha labari a filinmu na Girke-girken Azumi.

Kayan hadi

– Kifi

– Attarugu

– Albasa

– Tafarnuwa

– Sinadarin dandano

– Garin curry

– Gishiri

– Man gyada

Yadda ake hadawa

– A wanke kifin a gyara shi sosai, sai a dora tukunya a kan wuta, a zuba kifin da kayan kamshi da kayan dandano da tafarnuwa da sauransu.

– A zuba ruwa kadan sai a bar shi ya dan dahu kadan, sai a sauke.

– A kwashe ya sha iska sai a saka a turmi a daka shi har sai ya daku yadda ake so, a kwashe a ajiye a gefe.

– Sai a daka attarugu da albasa a hada da kifin a gauraya sosai.

–  Zuba sinadarin dandano da garin curry a ciki sai a jujjuya su hadu sosai.

– A dora tukunya a wuta sai a zuba man gyada kadan a soya yadda ake so.

Shi ke nan sai ci.