Barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Tare da fatar ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa mai launi-launi.
Ina so uwargida ta gane yadda ake irin wannan girki kuma abu ne mai sauki da za ta iya yi a gidanta, ba sai ta je gidan biki ba ko gidan da ake sayar da abincin zamani.
- Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigar Zamfara, Alhaji Auta
- An rufe coci mai shekara 220 saboda karancin masu ibada
Wannan girki dai ko talaka zai iya yi domin ba wani abu mai tsada za a sa a ciki ba, sai dai in ana son kawata shi. Abubuwan da za a bukata:
- Shinkafa
- Kaza
- Attarugu
- Koren attarugu
- Albasa
- Magi
- Kori
- Tumatur
- Launi na girki (food colour)
Yadda ake yin hadin: A tafasa shinkafa sannan a tsame a matsami a wanke da ruwa sai a ajiye a gefe.
Bayan haka sai a silala kaza da albasa da gishiri kadan har sai ta yi laushi yadda ruwan kazar zai bushe a jikinta.
Sai a yanka albasa da tumatur sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.
Sai a zuba man gyada kadan a tukunya bayan man ya yi zafi sai a zuba albasa da tumatiri da jajjagen attarugun sannan a dauko launi na abinci kore a zuba tare da zuba ruwa kadan, idan ya tafasa sai a zuba shinkafa kadan har sai ta nuna.
A sake yin irin wannan hadin da kowane launin da ake so na abincin, sannan a zuba shinkafa ta nuna. A soya kaza a dora a kai.