✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dafa dambun Kuskus

Sallama gare ki uwargida yaya fama da tarbiyyar yara? Allah Ya ba mu sa’a wajen sauke nauyin da ke kanmu. A yau na kawo muku…

Sallama gare ki uwargida yaya fama da tarbiyyar yara? Allah Ya ba mu sa’a wajen sauke nauyin da ke kanmu. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar dambun Kuskus tare da fatar za a gwada wannan girkin ga maigida ko baki. Za a iya cin wannan girki bayan an dawo daga aiki ko a ci a lokacin karin kumallo. Yana da kyau maigida ya rika ganin canji a girkin da uwargida take dafawa musamman a wannan lokaci na damina.

Abubuwan da za a bukata

  • Kuskus
  • Koren wake (green beans)
  • Albasa
  • Attarugu
  • Hanta ko nama
  • Magi
  • Kori
  • Man gyada

Hadi

A samu hanta ko nama a dafa ta har sai ta yi laushi sosai. Sannan sai a samu albasa da attarugu a yanyanka su su ma kanana. Bayan hanta ta nuna ita ma a yanka ta kanana. Kada a zubar da ruwan da aka tafasa hantar  ko naman. Ana so a ajiye a gefe saboda dafa Kuskus din da shi. A dauko ruwan nama a zuba a kan danyen Kuskus da magi da kori da attarugu da albasa da man gyada. Sannan a juya su kafin a samu leda a rufe da marufi. Sai a jira na tsawon minti biyar. Sai a sauke.

Za a iya sanya zogale ko alayyahu a cikin wannan girki domin dada armashi da kuma gardi. Lallai idan maigida ya ci wannan girkin sai kunnensa ya yi motsi.