✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake chocolate milkshake

Jama’a barkanmu da wannan lokaci tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau a filinmu na girke-girke mun kawo muku yadda ake yin chocolate…

Jama’a barkanmu da wannan lokaci tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

A yau a filinmu na girke-girke mun kawo muku yadda ake yin chocolate milk shake… daya daga cikin kayan sha na marmari.

 • Abubuwan da ake bukata
 1. Chocolate chips
 2. Garin koko
 3. Kankara
 4. Sukari
 5. Madara
 6. Chocolate syrup
 • Yadda ake hadawa
 1. A hada chocolate chips, madara, garin koko, sukari, da kankara a zuba su a blender.
 2. A markada su sannan a juye a kofi.
 3. Sai a yaryada chocolate syrup din a cikin kofin da za a sha kafin a zuba markaden a ciki.
 4. Za a iya zuba chocolate syrup din a saman markadaen idan an gama.

Wannan shi ne yadda ake hadda chocolate milkshake cikin sauki.

A sha dadi lafiya.