Abubuwa sun kankama inda manyan baki suka hallara domin shaida bikin ba wa Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu sandar mulki.
Dubun dubatar mutane da suka hada da sarakuna, kusoshin gwamnati, ‘yan siyasa, attajirai, mawaka, matasa maza da mata sun yi wa Birinin Zariya tsinke domin halartar gagarumin bikin.
- Sarkin Zazzau ya kai ziyarar farko ga Sarkin Musulmi
- Takaitaccen tarihin Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli
- Kotu ta amince a ba wa Sarkin Zazzau sanda
- Yadda ake gudanar da sha’anin mulki yau da kullum a Masarautar Zazzau
Nadin Sarki Ahmadu Bamalli na zuwa ne shekara 100 rabon da a yi irinsa a gidan da ya fito daga cikin gidajen Sarautar Zazzau —Gidan Katsinawa.
Rabon Gidan Katsinawa da rike Sarautar Zazzau tun zamanin kakakn Sarki Ahmad Bamalli, wato Sarkin Zazzau na 13, Sarki Alu Dan Sidi wanda ya rasu a shekarar 1920.