✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake bautar da mata a gidajen Gala

Rashin sanin ciwon kai da sha’awa suka kai ni solo kuma na yi da-na-sanin shiga harkar.

Talatu (ba asalin sunanta ba ne) ta baro Jiharta ta asali, wato Jihar Bauchi zuwa Abuja bayan wani dan sabani domin neman kudi.

Amma bayan dogon lokaci a Abuja, yanzu Talatu tana fama ne da neman na abincin da za ta sa a bakin salati da na ’yarta.

“A gidan gala ana bautar da mata ne kawai,” inji ta cikin tattausar murya.

Gidan Gala ko Gidan Dirama ko Solo wani tsarin nishadantarwa ne dadadde da ake gudanarwa a wasu birane, musamman a yankin Arewacin Najeriya, amma yanzu yake neman karade kasar baki daya, musamman a yankunan da Hausawa suke a Kudancin kasar nan.

Kamar yadda tsarin yake tun asali, matasa ne maza da mata kan taru, suna gabatar da wasan kwaikwayo na barkwanci da kadekade da raye-raye, domin nishadantar da mutane.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa ba nishadantawar kawai ake yi ba, ana gudanar da wasu harkokin a bayan fage.

Ga bako, waje ne kawai da zai ga an sa kida, mata da maza su yi rawa ana yi musu liki, daga nan a tashi. Sai dai bayan wasan, akwai wasan bayan wasa.

Binciken Aminiya ya gano cewa ana bautar da mata a gidaden ta hanyar duka da wulakanci iri-iri musamman idan ba sa kawo kudi. Sannan matan suna koyon shaye-shaye da zinace-zinace.

Haka kuma akwai zargin cewa gidajen suna samun goyon bayan ’yan sanda da wadansu jami’an tsaro domin ci gaba da gudanar da harkokinsu.

Ziyara gidan gala

A Kaduna, akwai gidajen gala da dama. A yankin Magadishu da ke kusa da babbar hanyar Ahmadu Bello da ke cikin Kaduna, akwai akalla gidajen gala guda uku.

A Abuja kuwa, akwai gidajen gala a yankin Jabi da Nyanya da Kubwa da Zuba da sauransu.

A Gidan Gala na ’Yan Doya da ke Kaduna, wakilinmu ya biya kudin shiga, amma babu tikiti.

Da shigarsa ya tarar da maza da mata matasa da manya a zazzaune. Wadansu suna shan sigari. Amma daga gani, akwai alamar wadansu suna yin shaye-shaye, kuma akwai alamar rashin kan-gado a tattare da su.

Da karfe 4:00 na yamma aka fara wasa har zuwa karfe 6:00, inda mai gabatarwa ya sanar da cewa za a tafi hutu domin a yi Sallar Magriba.

A Gidan Gala na Galazy. Akwai tikitin shiga, wanda wakilinmu ya saya a kan Naira 200.

Wata budurwa da wakilinmu ya gani a ciki ta sanar da shi cewa karfe 8:00 na dare ake fara wasa, inda suka tattaunawa kamar haka.

“Na ga kina shan sigari, a ina ake sayarwa. A can ne,” inji ta, inda ta yi nuni da wani dan kanti. Wiwi fa da sauran kayan ‘caji’ ana samunsu? A’a, ai irin wadannan ba a fili ake sayarwa ba.”

Da misalin karfe 7:45, ’yan wasan suka fito dukkansu a wani abu da ake kira ‘All Artists’. Daga nan aka bukaci su gaishe da masu kallo, sannan su biya kudin wanka.

Daga nan wadda ta biya kudin wanka za ta fito ta zabi wakar da za ta hau ta yi rawa. Haka za a yi wa kowace ’yar wasa.

Dole ki rika bin maza domin ki samu kudi – Rabi

Rabi wata matashiya ce mai kimanin shekara 22 da ta ce ta yi shekara 7 tana harkar solo.

A cewarta, “Na taso ban samu kulawa sosai ba, kuma ina da bukata da yawa, ba a iya biya min a gida saboda rashi. Haka na fito neman kudi, sai a haka har na fara zuwa gidan solo.

“Wata rana wani Alhaji ya zuba min kudi, da aka tashi sai ciyaman dinmu ya ce in je in yi masa godiya. Na je, sai Alhajin ya ce in ba shi lambata, sai na ce masa ba ni da waya. Washegari ya dawo, ya kara zuba min kudi, sannan ya ba ni waya da layi. Nan ne ya ce min zan bi shi. Na ce masa ba bin maza na fito ba, kudi na fito nema. Sai ya ce min ba a fada min yadda ake yi ba ne? Ya ce sai in amince zan bi shi, amma na ki. Daga nan sai ya daina sa min kudi. Aka sa gasa, shi da yake sa min kudi har in lashe, sai ya ki saka min kudin.

“Sai wata kawata ta ba ni shawara cewa dole in riga bin sa idan ina so in ci gaba da samun kudi. Idan ba na bin sa, ba zan rika samun kudi ba. A haka ne na fara bin sa, ranar farko da na bi shi, ya ba ni Naira dubu 20. Daga nan na ci gaba,” inji ta.

Ta ce, “Duk kudin da kuka samu a saman dandamalin rawa, na shugabanninku ne ko da kuwa nawa aka lika miki. Sai dai kudin da zai rika biyanki. Amma idan kika bi namiji, ko nawa kika samu naki ne.

“Haka na ci gaba da bin maza ina samun kudi, sannan idan an sa gasa su zo su yi min liki, in lashe. A haka har na saba da bin maza.”

Game da ko shugabanninsu suna sane, sai ta ce, “Ai sun san namiji ba zai sa miki kudi har Naira dubu 100 zuwa sama haka nan ba. Duk ciyaman yana kama wa ’yan wasa haya. Za ka ga an kama gidan da suke kwana. Tsarin shi ne, kada ki kawo namiji gidan, amma duk inda za ki je a waje, babu ruwansu.”

Sai dai ta musanta cewa matan sukan fito su bi maza sannan shugabanninsu su kwace musu kudi, inda ta ce, “Ba a haka gaskiya. Sai dai idan shi ma yana nemanki, kila za ki iya yin haka. Kuma ko hakan, me zai nema a wajenki. Sai dai idan kuna soyayyar ’yan solo wato wanda kuke wasa da shi, za ki iya fita ki samo kudi ki ba shi.”

Game da batun kamen ’yan sanda kuwa cewa ta yi, “Idan ciyaman ya san abin da yake yi yana biyan ’yan sanda kudi. Sojoji dai suna zuwa kallo. Amma an taba kama ni sau daya a Kaduna. Sai aka zo aka yi belinmu. Amma bayan wannan, ba a kara kama ni ba. Kuma ban gani ba. Kuma wannan waje ne da za ka ga mutane masu shaye-shaye sosai. Kuma ’yan daba na shigowa. Da sauran marasa ji.”

Yadda na koyi shaye-shaye

“Gaskiya kusan rabi da kwata na ’yan solo suna shaye-shaye. A can na koyi shaye-shaye. Amma wadansu ba sa yi. A gidan wasa ma akwai ’yan sanda da suke zuwa cikin kayan gida, idan suna kallon rawa, suka ga alama suna zuwa suna yi wa ciyaman dinmu magana cewa mun yi shaye-shaye,” inji ta.

Game da yadda suke samun kayan shaye-shayen, sai ta ce, “A boye ake sayarwa. Hukuma tana shigowa ai. Ka ga gidan da nake wasa yanzu, da ana shan Shisha da sauransu a fili. Amma yanzu an hana. Amma ana shaye-shaye, sai dai ba a fili ba ko kuma a shiga bayi, a buya, a sha.”

Game da zargin shugabanninsu na nemansu, ta ce, “Suna nema mana. Idan ya nemi yarinya ta ki yarda, za ta yi bakin jini. Idan wani abu na ci gaba ya zo, ba zai ba ta ba. Sannan sukan ba abokansu, musamman idan ya fuskanci zai sa kudi.”

Sai dai ta ce tana tunanin sun fi shugabannin samun kudi, a cewarta, “Idan kudin da namiji ya lika miki ne rabawa za ku yi, amma idan kika bi shi gida, naki ne ke kadai. Ka ga mata suna samun kudi. Harkar solo babu amana, za ka ga matan suna bin maza da yawa suna samun kudi. Idan kuma kuka saba da wani, ko ba ki bi shi ba, zai kira ki ya ba ki kudi.”

Kan batun daukar ciki da zubar da shi, ta ce, “Yawanci ana samun haka ne a soyayya da dan solo. Idan kin san me kike yi, ai ba za ki bari ki yi ciki ba. Amma idan ana soyayya da dan solo, a kan zama kamar mata da miji ne.”

Sai ta ce, “Idan kina soyayya da dan solo, za ki iya fita ki je ki samo kudi. Ki ba shi, sannan ya dake ki, ya zage ki, sannan ya kwanta da ke. A irin wannan ne ake samun ciki. Amma a inda nake wasa, ciyaman dinmu ba ya so, amma dai anayi. Na sha raka kawayena su zubar da ciki.”

Kan batun ko ana yi musu asiri, Rabi ta ce, “Kwarai kuwa ana yi. Idan suka fuskanci kina kawo kudi, ai ba za su bari ki bar gidansu ba. Amma idan ba ki kawo kudi, da kansa zai kore ki. Akan yi tankade da rairaya. Ka ga ciyaman ya tara mata ya rairaye wadansu, ya ba su kudin mota su tafi.”

Dangane da ko za ta iya tuna maza nawa ta bi, cewa ta yi, “Gaskiya ban san nawa ba ne adadinsu. Maganar gaskiya kudaden da nake samu a bin mazan nake samu. Amma ban taba yin soyayya da dan solo ba, saboda ni ba zan iya bin namiji in samu kudi in ba wani kato ba.”

A karshe Rabi ta ce tana da burin barin solo ta je ta yi aure ta zauna a gidan mijinta duk da ta ce ba za ta auri wanda yake zuwa gidan solo ba, saboda a cewarta ba za su zauna lafiya ba.

Yadda na shiga harkar solo -Maryam

Maryam, matashiya ce da ta kwashe shekara 8 tana solo a garuruwan Maiduguri da Abuja da Fatakwal da Abiya.

A cewarta, “Na shiga solo ne ta sanadiyar kawata. An ja ra’ayina ne cewa zan fara fim. Ashe ba fim din ba ne. A Maiduguiri na fara. Da na ce tunda ba fim ba ne, zan koma, sai ciyaman din ya ce in ba shi kudin motar da ya bayar aka kawo ni. Ni kuma ba ni da kudin komawa gida, haka na hakura. Kan ka ce kwabo na saba.

“Na samu kudi, amma na sha wahala. Ba za ka samu kudi sosai ba, sai kina bin maza. Idan mutum ya sa miki kudi dole ki bi shi, idan kika ki kuma zai iya jawo miki wulakanci. Amma ciyaman dina na Maiduguri sunansa Nura shi ba ya yarda dan kallo ya taba masa ’yan wasa.

“Daga Maiduguri da na ji dadin harkar, sai na tafi Fatakwal daga can kuma na shiga Abiya. Daga Fatakwal na koma Abuja. A gidan solo ne na koyi shaye-shaye. Daga shan taba har na kai babu abin da ba na sha.

“A ranar farko ne wani ya ce in bi shi, na ce masa a’a, da ya ji haushi sai ya fara biyan kudi ana min wulakanci. Aka zuba min bakin mai da ruwa da sauran wulakanci. Idan namiji yana jin haushi, zai sa a yi miki wulakanci a gaban mutane. Ciyaman ko mai gabatarwa zai ba kudin. A wani wajen har wurin kulle mutum ake da shi kamar keji da ake sa mutum. Aka sa ni a cikin kejin, har wani ya lura cewa ban saba ba ne, sai ya zo ya yi belina.

“Da na ga wulakancin ya yi yawa. Zan sa kaya masu kyau a bata min, sai na fara bin mazan saboda wadanda kike bin ne za su rika zuba miki kudi har ki samu ’yanci a gidan. Da haka na gane, ni ma na fara bin maza. Wani zai zo kai-tsaye ya ce miki kwanciya yake so ya yi da ke. Wadansu kuma suna so ku yi soyayya, ku yi zaman dadiro.”

Wahalar da ban taba mantawa

“Akwai wani saurayi da ya kama min daki a Fatakwal a wani waje da ake kira Elem Junction. Ya kama dakin ina kwana, idan ya zo mu kwana tare. Amma ba a nan yake zama ba. Ina dakin ne wata rana ’yan NDLEA suka kama ni, suka tafi da ni. Ina can ne na kira shi, ya ki zuwa. Nan hankalina ya tashi. Bayan na dawo da kyar, sai gari ya kaure da fada. Shi kuma saurayina ya ki zuwa gani a wani waje da ake kira Obadu Junction lokacin fadan Obibo, an kashe mutane da dama. Nan na kira babana na ce masa ya yafe min na zaci mutuwa zan yi. Saboda har yanzu a gida ba a san ina solo ba, cewa na yi aiki nake yi.

“Wata wahalar da ban mantawa kuma ita ce wani ciyaman da ya neme ni. Neman matansa ya yi yawa, kuma idan yana nemanki, babu dan kallo da zai neme ki. Zai takura ki. Haka ya sa aka kama ni, zai buge ni. Kuma yana jizga ni,” inji ta.

Game da ko rayuwar bauta suke yi, cewa ta yi, “Rayuwar bauta ce mana. Kai za ka tsaya ka yi rawa a samu kudi kamar Naira dubu 100, amma bai wuce a ba ka Naira 500 ba. Ka ga ke nan shi muke yi wa wahala. In da za ka samu kudi shi ne idan ka bi namiji. Amma a gidan wasa in Naira miliyan aka lika maka, kudinsa ne.”

Kin fara wasa kina karama sosai, shekara 16, babu doka ce. “Babu wata doka ta duba karamar yarinya. Su dai kawai ki yi wasa, idan ’yan wasan suna son ki shi ke nan.”

Dangane da zargin ana asiri, “Wallahi ana asiri. Idan (mai gidan solo) ya lura kina kawo masa kudi, zai yi miki asiri ya daure ki. Ko kin tafi, sai kin dawo. Da wahala ki tafi, ko kin tafi sai kin dawo. Har ’yan kallon ma, ana musu. Da zarar ka fara zuwa, ka rika zuwa ke nan. Wadansu suna shekaru ba su je gida ba,” inji ta.

Batun dauka da zubar da ciki, “Ban taba yin ciki ba. Amma wadansu sun yi da yawa. Wadansu suna zubarwa wadansu suna haifewa,” inji ta.

A karshe ta ce tana da burin Allah Ya yaye mata harkar solo domin a cewarta, “Da yawa sun mutu. Jana’iza ma a cikin wulakanci ake yi musu.

Bautar da mata ake yi a gidajen gala —Talatu

Talatu tsohuwar ’yar solo ce da ta yi ritaya bayan kwashe shekaru tana wasa a Abuja da Bayelsa.

“Rashin sanin ciwon kai da sha’awa suka kai ni solo. Duk abin da kake magana na bayan fage yana faruwa. Ni dai inda na yi wasa kamar yadda na sani, idan namiji ya zo ya miki likin kudi. Wannan ra’ayinki ne, babu ruwan ciyaman. Idan kin ga dama ki bi shi, idan ba ki dama ba, ki ki. Shi dai ya zo ya miki asarar kudi. Akwai wadanda ma idan namiji ya miki asarar kudi, idan ba ki bi shi ba, yakan zama rigima a tsakaninsu da ciyaman. Kuma akwai wadanda idan namiji ya yi wa wata mace asara, sukan ce ta bi shi.

“Na yi wasa a gidan Shagari Billa a ’Yan Lemu da ke Abuja. Sai wani gidan solo a Bayelsa mai suna Gidan Jogodo. A zamana na ga abubuwa da dama. Zamantakewa da abubuwan da ba za ka taba ganin su ba a duniya sai a irin gidajen. Za ka ga idan namiji da mace sun samu matsala ko fada, za ka ga ta fara shaye-shaye. Ko idan mace ta ga saurayinta ya kula wata su fara fada. Ko idan mace ba ta samun beli bayan sun gama rawa, sai ciyaman ya sa a buge su.

“Wadansu mata da sukan ce idan namiji ya yi musu beli ciyaman ke cin kudin, don haka duk wulakancin da za a yi musu, kada ya ba da kudin beli. Sai a yi musu wulakanci a gama, su hadu a waje ya ba su kudin.”

Zamana a Bayelsa

“A Gidan Jogodo a Bayelsa ba zan taba mantawa ba, wani ciyaman ya ce in je wasa na ce ba zan iya zuwa ba, sai ya kama ni da duka, har ya kusa fasa min ido. Na gudu na bar gidan, ina da wani saurayi soja na kira shi, shi ya kai ni asibiti.

Shawara ga ’yan solo

“Shi ya sa na ce maka wadda ta san ciwon kanta ba za ta yi solo ba. Abu ne na bautarwa gaskiya. Abu ne fa zai zama kina wahala wa wani kato, ke sai dai ki yi ta wahala shi yana amfana da kudin, a gidan wasa ana iya samun Naira dubu 200 zuwa sama a kullum. Sai dai na abinci da suke bayarwa a kullum. Na yi da-na-sanin shiga harkar solo. Shawarata ita ce su bari kawai. Gaskiya duk yaudara ce kawai da cutar da mata. Wani ne zai yi ta amfana da kudin da kike samu. Wani zai yi arziki da su kawai. Da ma ki yi solo gara ki yi zaman kanki, ki rika samun kudinki na kanki,” inji ta.

Yadda na kirkiri Gala – Lilisco

Shu’aibu Lilisco fitaccen tsohon dan wasan Hausa ne, wanda shi ne ya canja salon wasan gidan dirama zuwa wannan tsari da ake yi a yanzu.

A tattaunawarsa da Aminiya ya ce, “Mun fara gala ne a 1999. Ni na sa sunan wasan gala. A wannan lokaci wasan dabe ake yi, sai rawar koroso. Ni kuma a lokacin na fitar da wani tsari na raye-raye a fina-finan Hausa. Ni ne mutum na farko da na fara rawa a fim din Hausa a wani fim dina mai suna ‘Dashen da Allah ke so’ da ni da Sani Musa Mai Iska. Wannan ne fim na farko da aka fara rawa da waka ta zamani.

“Bayan wannan sai na shirya wani wasa a Sinimar Lale. A wannan wasa da muka shirya sai muka sa masa sunan Gala. Da Koroso ake yi da dirama, sai ni na sa aka kawo min kayan sauti na sitidiyo. Sai na fara hawan waka a bainar jama’a. Sai mutane suka fara sha’awa. Bayan mun gama, sai jama’a suka sa aka sake. Sai da muka yi kwana uku muna yi. Wannan ne ya yi tasiri, sai wadansu suka fara daukar wannan dabarar. Wannan shi ne asalin wasan Gala da ake yi a yanzu.

Ya kara da cewa, “Mun assasa Gala ce domin nishadantar da mutane. Za ka ga an fi yi da yamma domin lokacin an tashi daga kasuwa ko wajen aiki da sauransu.”

Game da batun ko an sauka yanzu daga yadda suka faro, sai ya ce, “Gaskiya akwai bambanci. A da ka ga ko kayan ma sun bambanta, domin ana suturta jiki, amma yanzu har gajeren wando matan na sakawa da kuma atamfa ake sakawa. Yanzu ma ana sa kaya matsattsu. Rawarmu a da akwai tazara, amma yanzu a hade ake. A da, muna lura da addini da al’ada, amma yanzu an kawar da su, nishadin kawai ake yi.”

Game da zargin gidajen sun zama matattara badala, Lilisco ya ce, “Eh, akwai irin wadannan matsaloli a wasu gidajen gala. A wasu gidajen idan ka shiga za ka yi tunanin kamar an bude bangare ne na shaye-shaye. Wannan laifi ne na shugabannin. Ya kamata daga lokacin da ka bude waje domin neman arziki, idan ana harkar kayan maye, sai ka je ka yi magana ka hana. Amma yawanci shugabannin ba sa haka. Sakacinsu ne ya kawo haka.”

Shawara

“Shawara ita ce dole shugabannin su tashi tsaye su cire son zuciya. In son samu ne ma, ya kamata su taimaka wa matan ta hanyar tambayarsu kai kun zo nan ne da sanin iyayenku. Idan kuma ba su sani ba, ya kamta su dauke su, su kai su wajen iyayensu su fada wa iyayensu abin da suke yi. Idan iyayen sun sani, shi ke nan. Idan ba su sani ba, su fada musu. Idan ba su yarda ba su dawo musu da su.

“Idan kuma iyayen sun aminta da su yi, to shugabannin su yi kokari su taimaka musu wajen tara musu kudi, su ba su shawara cewa kada su bari su kare a wasan. Su rika ba su shawarar su koma su yi aure. Sannan su lura da shaye-shaye. Sannan a rika lura da mu’amalar masu zuwa gidan da su. A lura da su wane ne suke mu’amala da su kamar barayi da sauransu,” inji shi.

Ba kara-zube muke ba – Shugaban Gidan Gala

A tattaunawarsa da Aminiya, Shugaban Gidan Gala na Freedom Theatre da ke Apapa a Jihar Legas, Alhaji Mamuda Akashe ya ce suna da tsare-tsare masu tsauri.

A cewarsa, “Kowane gidan gala na da shugabanni. Idan za ka bude, za ka yi rajista da Ma’aikatar Al’adu ko ka samu wadanda suke harkar ka ce za ka bude. Idan ba ka iya harkar ba, ba za ka iya budewa ba.

Ya ce, “Idan an yi bako, akan tambaye shi, shi wane ne, kuma daga ina yake. Idan ya taba wasa, sai a ji daga wane gida yake. Dole sai an nemo lambar gidan wasan da ya baro a binciki halinsa. Idan yana da hali na banza, sai an gano. Daga nan sai a zauna a fada masa tsare-tsaren gidan namiji ne ko mace. Karfe kaza ake fara wasa karfe kaza ake tashi. Mu ba a shaye-shaye, kuma ba a fita sai an nemi izini. Kuma ba ma daukar dan wasa sai mun binciki daga inda ya fito. Mu binciki iyayensa da wadanda ya sani a unguwarsu. Sai mun buga waya mun tabbatar daga inda ya fito. Idan ba a dauki wannan mataki ba, sai wani abu na rashin lafiya da mutuwa ko hadari ya same shi, babu yadda za a yi da shi.”

Game da shaye-shaye, ya ce “Duk shaye-shayen yaro bai isa ya yi mana shaye-shaye ba. Kuma idan muka gane mutum yana yi, ba zai yi mana wasa ba. Idan ka yi bincikenka ka gama. Sannan bayan ’yan wasa sun koma masaukin da muka ba su, idan sun yi wani barikinsu a bayan fage, wannan su suka sani. Amma mukan bibiyi lamarinsu, mu ba su shawara idan mun lura suna wasu harkoki da ba su dace ba. Kuma muna da tsari na babu wanda ya isa ya yi wa ’yar wasanmu wulakanci. Kuma ka ga yanzu haka a gidan wasanmu mun aurar da mata sun fi goma. Ni kaina na je har Nijar, na hada auren wata yarinya da wani ya gani yana so a nan gidanmu. Don haka, ba kara-zube muke ba.

“Kiran da zan yi ga wasu gidajen wasan shi ne su gyara. A wasu gidajen wasan gaskiya suna mayar da yara kamar awaki. Za ka ga wasu gidajen wasan suna karbar kudi a kan yaran. Wadannan yaran wata rana matan wadansu ne ko iyayen wadansu. Kamar ka bude kamfani ne sun zo suna aiki a ciki, don haka a daina bari ana wulakanta su. Ka auna idan ’yar uwarka ce, yaya za ka ji. A rika yi musu addu’a da ba su shawara Allah Ya kawo musu miji su yi aure su bar harkar. Shugabannin su san darajar ’yan wasa. Akwai shugabannin da suke tilasta wa ’yan wasa su rika bin maza masu ba su kudi. Mu gaskiya a wajemu ba a isa ba. Babu wanda ya isa. Kuma muna da likita da yake lura da matan da suke yi mana wasa. Idan za ta je gida, kuma mukan yi musu alheri sosai su je gida su dawo.”

Game da tallafin gwamnati, cewa ya yi, “Muna bukatar tallafin gwamnati. Ka ga yanzu haka muna wasan Koroso, sojoji suna gayyatarmu da biki kuma muna yin fim. Don haka, muna bukatar gwamnati ta sa mana hannu domin mu kara gyara harkar.”

Akwai bambanci tsakaninmu da su – Nura MC

Aminiya ta tuntubi Shugaban Masana’antar Fim ta Kaduna, Nura MC, inda ya ce a da ne suke tare, amma yanzu an raba gari. “Eh, a gaskiya a da can baya a iya sanina akwai alaka a tsakaninmu saboda farkon da aka fara yawancin ’yan fim din Hausa ’yan wasan gidan dirama ne wato ’yan wasan dabe. Daga baya bincike ya nuna da yawansu musamman matan masu zaman kansu ne, hakan ya sa aka fara kyamar harkar.

Da tafiya ta fara nisa, sai aka gano matsaloli, inda daga lokacin da fim ya zama babbar sana’a sai aka fara saka tsari inda ake rajista, wanda a cikin abin da ake bukata dole sai da sa hannun iyaye a ciki. Ta haka ne aka fara kakkabe wadanda suke zaman kansu aka koma amfani da wadanda suke fitowa daga gidan iyayensu su yi aiki su koma gida.

Ya ce, “Yanzu akasarin wadanda suke fitowa a fim ba sa so ana alakanta su da ’yan gidan gala dalili kuwa, yawancin ’yan gidan gala ana yi musu kallon wadansu irin mutane ne, kuma da yawansu in ka ce masu su zo su yi fim za su ce maka ba su iya ba. Kawai su dai sun fi kwarewa ne wajen iya bin waka da rawa.”

A karshe ya ce, “A gidan Gala mukan dauko ’yan rawa domin a nan ne aka fi samun kwararru maza ’yan rawa.

Akwai ’yan sandan sirri a gidajen Gala – ’Yan sanda

Aminiya ta nemi jin ta bakin ’yan sanda game da yadda suke lura da gidajen na gala. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammad Jalige ya musanta zargin cewa ’yan sanda suna karbar na goro, inda ya ce akwai ’yan sandan sirri a gidajen.

A cewarsa, “Muna kai samame a gidajen gala saboda barayi da marasa gaskiya suna buya a gidajen. Sannan akwai masu sayar da miyagun kwayoyi da suke zuwa gidajen kasancewar masu tu’ammali da miyagun kwayoyi suna zuwa wajen, sai suke zuwa su ma domin su yi ciniki. ’Yan sandanmu na sirri suna zuwa cikin kayan gida. Duk wanda ya aikata wani laifi ana kama shi, a bincike shi a mika shi kotu. Akwai mutanenmu a wajen sosai.”

Game da zargin cewa suna karbar na goro, sai ya ce, “Ai aikin dan sanda bai lalace haka ba. Ina karuwa take da abin da za ta ba ’yan sanda. Mu abin da muka sani shi ne muna tura ’yan sandanmu na sirri suna kasancewa tare da su, inda a nan ne suke zakulo batagari a cikinsu. Na yi aiki a inda muke zuwa sintiri a irin gidan, inda mukan yi kame. Idan gari ya waye mu tantance wadanda aka kama, mai laifi mu kai shi kotu, wanda bai da laifi mu sake shi. Wani lokaci ma da safe sai ka ga wadanda kuka dade kuna nema a cikinsu. Akan samu wani ya yi laifi ya gudu. Sai mu kama su a wajen. Amma babu maganar karbar wani abu.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Hukumar NDLEA, kan zargin sha da fataucin miyagun kwayoyi, amma hakan bai samu ba.

Wannan labarin Gidauniyar Daily Trust da MacArthur Foundation suka dauki nauyinsa.