Haramta holewa a gidajen Gala da sauran wuraren rage dare da Hukumar Hisbah ta ce suna kara habaka ayyukan lalata ya janyo cece-kuce a Jihar Jigawa a tsakanin wadanda haramcin ya shafa.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da Tarihi da Raya Al’adu ta Jihar Jigawa ta sanar da hukumar Hisban cewa ta sanya dokar haramta ayyukan gidajen Gala da sauran wuraren kada-kade da raye-raye kamar yadda ta bukata.
- Rikicin Gaza: Sheikh Dahiru Bauchi ya ba wa Falasɗinawa Naira miliyan 100
- An kafa dokar hana fita bayan harin barikin soji da fasa gidan yari a Saliyo
Shugaban kungiyar matasa ’yan dirama da wasan kwaikwayo ta Najeriya reshen Jigawa, Kawu Birnin Kudu, ya ce idan aka ba su dama za su iya amfani da sana’ar nishadi wajen rage yawan ta’asar karuwanci a jihar har ma da samar da kudaden shiga ga gwamnati domin inganta tattalin arzikin jihar.
Kawu Birnin Kudu wanda guda ne daga cikin masu shirya wadannan taruka na nishadi da kade-kade, ya ce sun yi tsammanin gwamnati za ta yi laakari da muhimmancinsu ta fuskar tattalin arziki maimakon hana su harkokinsu.
A cewar Kawu wanda aka fi sani da KKRK, harkokinsu suna inganta ayyukan nishadi a zamantakewa sabanin yadda wasu suke tunani.
Ya ce mazauna garin da masu kawo ziyara sukan samu saukin huce damuwarsu a wuraren nishadin bayan sun kwaso gajiya a wajen sana’o’insu.
Ya kara da cewa, harkokinsu suna ba da gudummuwa wajen janye damuwa a tsakanin matasa ta hanyar debe musu kewar da hana su fada wa cikin wasu ayyuka na bata-gari.
A yayin da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamandan Hisba na Jigawa, Mallam Adamu Musa, ya ce har yanzu ba a fara dakile irin wadannan cibiyoyi na gidajen Gala a fadin jihar ba, amma tabbas suna aiki kafada da kafada don rage munanan dabi’u.
Mazauna Dutse, babban birnin Jigawa, sun bayyana ra’ayoyinsu game da wannan batu, inda wani Bala Adamu ya ce ya ji dadin yadda hukumar Hisbah ta tsayar da ayyukan gidajen Gala a Dutse, yana mai cewa a kullum suna ganin sabbin fuskokin mutane wanda yakan haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kara daukar matakai domin tabbatar da hana gudanar da ayyukan gidajen Gala baki daya a fadin jihar.
Shi ma wani mai suna Is’haq Ibrahim mazaunin Dutse, ya ce, yana murna kuma yana bakin ciki a lokaci guda, domin kuwa hana ayyukan gidajen Gala zai dakile kofar nishadi da mutane ke shagaltuwa da ita da zarar sun taso daga wurarensu na aiki.
Ya ce a yanzu da aka sanya wannan doka, babu wani wurin shakatawa da ma’aikata za su samu su huce damuwa da gajiya sai kurum su koma gida su zauna tiris.
Ya kara cewa, gidajen Gala suna kara bunkasa harkokin kasuwanci sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, sjhi ne yadda gidajen Galar ke kara janyo kwararar baki da hakan yana barazana ga tsaro.
Wadansu masu ruwa da tsakin suna ganin cewa ababen da ke janyo lalacewa tarbiyya sun ta’allaka ne kacokam a kan rashin aikin yi da ya yi wa matasa katutu, inda suke kiran gwamnati da ta mike tsaye domin yi wa wannan tufkar hanci.