✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake azumi cikin talauci da tsadar rayuwa

Magidanta sun bayyana cewa bisa dukkan alamu sallar bana lami za a yi ta.

A daidai lokacin da aka fara ban-kwana da azumin bana, hankalin mutane musamman iyaye ya fara komawa ne kan kayan Sallah da abincin Sallah, a yayin da suke fama da ciyar da iyali a wannan lokaci da ake fama da hauhawar farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa.

Masu karamin karfi da dama suna kukan cewa abubuwa ba su taba tabarbarewa su zamo da wahala kamar haka ba.

Wadansu da wakilanmu a Kano da Kaduna suka zanta da su, sun bayyana yadda rayuwar yau ke gara su da kuma irin gwagwarmayar da suke yi wajen yin azumin Ramadan da tunanin da suke yi game da Sallah.

‘Akwai karancin tallafi’

Muhammad Sani, wani mazaunin Unguwar Dorayi ne a birnin Kano, ya shaida wa wakilinmu cewa tun kafin azumin da wahalar gaske shi da iyalinsa suke cin abinci sau biyu a yini.

Magidancin mai ’ya’ya shida ya yi korafin cewa, “Tsadar kayayyaki da yanayin tattalin arzikin kasa sun canja komai.

“Ba ni ne abin damuwa ba amma iyalina, musamman kananan yaranmu.”

Sai ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimaka wa talakawa, musamman a watan na Ramadan.

‘Kwana uku ba a dora tukunya a gidana ba a azumi’

Shi kuwa Jibrin Musa da ke zaune a Unguwar Sagagi a Kano, ya ce ya shafe kwana uku a jere ko tukunya ba a dora a gidansa ba.

Ya ce ya yanke shawarar ya rika ziyartar masallatai don neman taimakon abin da za su ci da iyalansa.

“Ina da mata daya da ’ya’ya shida; saboda matsin tattalin arziki da muke fuskanta mun cinye jarina tun kafin a shiga Ramadan, yanzu na rasa sana’ata,” inji Musa yana hawaye.

Ya kara da cewa, “Ina bukatar a taimaka min da sana’ar da zan rika yi don samun abin da zan ciyar da iyalina.”

A nata bangaren, Larai Mu’azu, wata gyatuma mai ’ya’ya bakwai wadda kan fita bara a titunan Kano kafin samun abin da za su ci, ta ce “Kafin Ramadan, ba mu iya cin abinci sau uku a yini.

“Sau biyu muke cin abinci a ranar da harka ta yi kyau, wasu lokutan kuma sau daya tak.”

Larai ta ce shekara daya ke nan da rasuwar mijinta, kuma ya rasu ya bar mata ’ya’ya bakwai ba tare da samun tallafi daga wajen wani ba.

Gyatumar ta ce yanayi ne ya tilasta mata shiga bara, tare da cewa “Babu wani tallafi da muke samu daga ’yan uwana.”

Ta ce, takan bi gidajen masu hali inda ake raba wa marasa galihu abinci kafin su samu abincin da suke buda-baki da shi.

Alhaji Sa’adu Yusuf, wanda dan kasuwa ne a Zoo Road Kano, ya ce, cinikin da yake yi a yini ba ya dauke masa hidimar gidansa.

Sai dai kuma, sabanin halin da wadansu ke fuskanta game da ’ya’yansu, Alhaji Sa’adu Yusuf ya ce shi dai ya taki sa’a domin nasa ’ya’yan kan tallafa masa gwargwadon hali idan sun fita sun roro.

‘Cinikina bai kai Naira 2,000 ba tun safe’

Lawan Maicarbi wanda yake sayar da carbi a Kano, ya ce “Akalla dai yin wannan kasuwanci ya fi zaman kashe wando.

“Tun safe zuwa kusan karfe 5:00 na yamma, ban yi cinikin Naira 2,000 ba.

“Dan cinikin da na samu shi muke lallabawa mu yi amfani da shi.

“Wasu ranakun ma ba na samun abin da zan ciyar da iyalina.”

Shi kuwa Muhammad Abdu, wani mai fama da nakasa sannan yana da mace daya da ’ya’ya hudu, ya ce baki dayansu sun dogara ne ga bara don samun abinci kasancewar ba su da sana’a ko wata tsayayyar hanya ta samun abin masarufi.

Ya ce, “Ba sona ba ne, na tsani bara amma yanayi ne ya tilasta min saboda abin da zan iya yi ke nan kawai.

“Ina fama da nakasa, na rasa hannuwana biyu sannan ba ni da wata madogara.”

Da kyar muke samun na sahur

Wani mazaunin yankin Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, mai suna Malam Mohammed Yusuf, ya ce akwai ranar da da kyar ya iya samun wake gwangwani biyu da ya kai wa iyalinsa aka yi budabaki da shi.

“A wannan lokaci na azumi kuwa, da kyar nake samun abin da za mu yi sahur da shi, amma da taimakon makwabtanmu muna dan samun abin kaiwa bakin salati lokacin buda-baki,” inji shi.

Ya kara da cewa, ala tilas ya bar ’ya’yansa suke tafiya aikatau don su samu abin da za su kula da kansu.

Wata mazauniyar Kaduna mai suna Hauwa Ibrahim, ta ce azumin bana ya zo a lokacin da jama’a suke cikin mawuyacin hali.

Ta ce kafin zuwan Ramadan, gidaje da dama suna fama ne da abin da za su ci, gidanta ma na daga cikinsu.

“Ni bazawara ce, mijina ya rasu shekara biyu da suka gabata, sannan muna da ’ya’ya biyar, tun bayan rasuwar dawainiyar kula da gida ta dawo kaina.

“Ban yi karatu ba sai dai nakan taba ’yar sana’ar da ba ta taka kara ta karya ba, don haka da zuwan azumin nan abin ba a cewa komai.

“Ba don agajin abincin da wata Kungiyar Mata Musulmi ta ba mu a unguwarmu Tudun Wada ba, da tuni yunwa ta kai mu ta baro.

“Hankalina ba a kwance yake ba, don kuwa ragowar abincin da aka raba mana ke nan zan girka, daga nan kuma ban san abin da zai biyo baya ba,” inji ta.

‘Lami za a yi sallar bana’

Babangida Abdulmumini Shehu mai gadi ne a Kaduna, ya bayyana cewa duk da akwai rashin kudi amma ya yi kokari ya dan yi wa yaransa dinkin Sallah.

“Allah Ya taimake ni na dan samu abin da aka yi wa yara dinkin Sallah daga ajiyar da na rika yi tun kafin azumi dinkin Sallah daga ajiyar da na rika yi tun kafin azumi.

“Yanzu abin da kawai ya rage min shi ne kudin sayen abincin Sallah domin a maganar gaskiya ana cikin wani hali sai dai kawai a ci gaba da addu’o’in Allah Ya kawo mana taimako,” inji shi.

Shi ma Malam Jafaru Madobi ya bayyana cewa saboda kuncin rayuwa da mutane ke ciki za su yi Sallah amma ba a cikin natsuwa ba.

“Ya ce shi a yanzu ta kayan abincin da za a ci a gidansa yake ba ta kayan Sallar yara ba.

“Za a yi Sallah ba a cikin natsuwa ba domin akwai ta’addanci, na biyu kuma mutane ba su da wadata, sannan ba su da inda za su je su nemo abubuwan da za su yi amfana da shi.

“Ni a da na fara sayar da safa ce ta gwamjo amma abubuwan sun lalace, yanzu mangoro nake zuwa sayowa a gefen kwalta domin idan ka sake ka shiga cikin daji an tafi da kai ke nan ko kana da kudi ko babu,” inji shi.

Game da ko yara za su samu kayan Sallah sai ya ce, “Tsakani da Allah ni fa ta abin da za a ci nake, ba ta abin da za a sa ba.

“Kuma irina suna da yawa a inda nake a yanzu.”

Shi ma Sadisu Usman Dan Hassan mai gwanjo a Kasuwar Barci cewa ya yi shi har yanzu bai yi kayan Sallah ba domin babu kudi kuma babu ciniki a kasuwa.

Ya ce a yanzu ta ciyar da iyalinsa kawai yake yi ba ta kayan Sallah ba.

“Babu kudi a hannun mutane abin dai sai hakuri domin a rayuwa idan ka ce za ka damu kanka sai ka janyo wa kanka wani ciwo.

“Abin da kawai ya fi a halin yanzu shi ne tawakkali.

“Allah Ke bayarwa kuma Shi ke hanawa, don haka dole mu yi hakuri da rayuwar da muke ciki a yanzu,” inji shi.

Shi ma Kabiru Ayuba, mai facin taya cewa ya yi, “Ka san yara duk halin da ake ciki na kunci iyayensu suna iya hakura da duk wani abu domin su ga sun yi musu sababbin kaya ko da masu araha ne.

“Haka muke fama duk da ana hannu-baka-hannu-kwarya muke yi musu.

“Ni yanzu ’ya’yana biyar, amma tun wata shida baya na fara ajiya domin hakan,” inji shi.

A nata bangaren, Malama Sakina Umar ta ce, “To yaya za mu yi da halin da muka tsinci kanmu.

“Yara ba su san babu ba; Dole duk yadda za ka yi ka fitar da su kunya.

“’Ya’yana uku, mahaifinsu kuma ya rasu ga shi ’yan uwa ma ba wani karfi ne da su ba.

“Mun yi sa’a ma akwai wadansu masu tallafa wa marayu sun ba mu kayan abinci da na Sallah.

“Ba don haka ba gaskiya ban san yadda zan yi da su ba a dai halin da ake ciki.”

Daga: Aminu Naganye da Sadik Adamu da Salim Umar Ibrahim, Kano, Maryam Ahmadu-Suka da Mohammad Yaba, Kaduna da Bashir Isah