Kabilar Badawa karamar kabila ce da ake samun ta a Gashuwan Jihar Yobe da kuma wani bangare na Jihar Jigawa.
Kabilar tana daya daga cikin kananan kabilun Najeriya da al’adunsu suke gab da bacewa, sakamakon tasirin da Hausa da addinin Musulunci da kuma cakuduwa da sauran kabilu da suka yi.
A wannan rahoto, mun tabo yadda al’ummar Badawa suke yin aure tun daga lokacin da saurayi ya ga budurwar da ya ji yana son ta da aure har zuwa lokacin da za a daura masu aure da kuma abubuwan da sukan biyo baya.
A tattaunawa da wakiliyarmu, wani masani dan kabilar Bade (Badawa) Dokta Gimba Gwayo, ya yi cikakken bayani game da al’adun aure na al’ummar Badawa.
Ya ce Badawa wata karamar al’umma ce da yawancin ’ya’yanta suke da kusanci da juna.
Ya ce mutane ne masu yawan zumunci a tsakaninsu, kuma ba kowane lokaci ba ne ake samun yanayin da za su kama neman aure ba, sai sun girma sun mallaki hankalin kansu ne za su nemi auren yarinya.
Dokta Gimba ya ce a al’adar Badawa, aure iri biyu ne: akwai auren kamu da kuma auren gargajiya da aka saba yi a Arewacin Najeriya.
“Ta bangaren auren kamu, akwai yarjejeniya da ake kullawa a tsakanin iyayen namiji da mace.
“Misali, idan aka yi haihuwa aka samu ’ya mace, kawar mahaifiyar jaririyar za ta yi abin da ake kira da ‘kamu,’ cewa ‘idan mace kika haifa to na kama wa dana,” inji Dokta Gimba.
Ya kara da cewa haka kuma abokin zumuncin mahaifin yaron, zai iya cewa “Idan har namiji aka samu na kama wa ’yata,”inji shi.
Ya ce wannan salon na kamu yana kara dankon zumunci da karfafa al’ummarsu.
Sai dai yaya batun zai kasance idan yaran suka taso suka ce ba su yarda da zabin kamu da aka yi masu ba?
Hajiya Fatsuma Musa ta ce “Ai ba ka isa ma ka ce ba ka so ba, saboda maganar iyaye ba ta tashi. Sai dai idan aka daura kuma zama ya gagara sai ku rabu.
Idan mace ce, sai dai ki yi ta gudu daga gida har iyaye su shiga tsakani a raba auren.”
Bayan an yi wa yaro kamu, idan saurayin ya fara girma zai yi rika yin wasu kananan hidimomi ga wadda aka kama masa.
“Shi yaron zai iya kai mata abubuwa kanana kamar lalle da kayan Sallah da sabulun wanka ko dan kwali.
“Duk wadannan hidimomin zai yi su kafin su yi aure ne,” inji Dokta Gimba.
“Idan yarinya ta isa sa kananan sutura, dangin yaron ne za su yi ta dawainiyar kawo mata ta rika sawa.
“Idan ta girma sosai, har ta iya sa riga da zani, iyayen yaron za su zo gidan yarinyar sa rana.
“Za su zo da ’ya’yan itatuwa kamar kanya da aduwa da dabino tare da goro. Goron da aka kawo, shi za a raba wa jama’a.
“A al’adance Badawa ba su sanya ranar aure idan ba a lokacin rani ba. Dalili shi ne asalin Badawa yawanci manoma ne da masunta kuma ba a cika noma ba a lokacin rani.
“Idan iyayen yarinyar suka ba da izinin yaro ya auri ’yarsu, to saurayin zai je gonar mahaifin yarinyar ya yi masa aikin gona. Wannan shi ake kira da ‘gayya,’” inji shi.
Ya ce, bayan an yi gayya, iyayen yaron za su je gidan iyayen yariyar tambayar nawa za su bayar da kudin sadaki. Bayan an yi yarjejeniya a tsakanin iyayen, an ba da sadaki sai a daura wa yaransu aure.
“Bukukuwan aure sun danganta da karfin iyayen.
“Kuma wadansu amaren sukan zauna a gidan iyayensu har tsawon shekara daya idan ba a yi masu biki (gara) ba, amma dole ne a kai amarya gidan mijinta na mako daya bayan an daura masu aure.
“Bayan haka, sai a dawo da ita gidan iyayenta ta zauna har a yi bikin,” inji Dokta Gimba.
Ya kara da cewa “Wadansu amaren har sukan haihu a gidan iyayensu kafin a yi masu biki, ya danganta da karfin gidajen.”
Wani dalili kuma da ke sa a bata lokaci wajen yin biki shi ne sa hannun da ’yan uwa da abokan arziki suke yi.
Sauran iyali sukan sa hannu a taimaka wajen shirye-shiryen biki.
Don haka, iyayen da suke aurar da ’ya’yansu sukan yi la’akari da sauran danginsu domin kara dankon zumunci.
Bayan an gama duk hidimar aure da ta kamata a tsakanin iyalan ango da amarya, sai amarya ta koma gidan mijinta, inda za su ci gaba da zama.
Ta bangaren abubuwan da ake yi yayin biki, akan samu wadanda ake hada bikinsu lokaci daya saboda yara su za su taso tare.