Ga bayani dalla-dalla, daga farko har karshe, kan yadda ake dafa alalar shinkafa.
Kayan hadi
- Shinkafar tuwo
- Nama ko kifi
- Man gyadda
- Manja
- Tattasai
- Attarugu
- Albasa mai lawashi
- Kori
- Thyme
- Kwai
- Magi
- Gishiri
Yadda ake hadin
– A wanke shinkafa a shanya ta bushe, sai a nika ta a a tankade.
– A samo roba mai zurfi a zuba garin shinkafar a cikin sai a zuba ruwa a kwaba kamar kwabin kullun kosai.
– A yayyanka dafaffen kwai a zuba a ciki.
– Zuba dakankken kayan miya, sai a yayyanka albasa da lawashi kanana a ciki.
– A zuba kayan dandano da man gyadda da man ja dadai yadda ake bukata.
– A marmasa nama ko kifi a zuba a ciki, sannan a zuba kori da thyme a juya soai kullun ya hadu sosai.
– Sai a samu gwangwani ko leda a zuba a cikin dai dai yadda ake so.
– Sanya tukunya a wuta sai a zuba ruwa a ciki.
– Idan ruwan ya tafasa sai a zuba kullin alalen a cikin, a rufe sosai da leda ko gyanyen ayaba.
– A bari a kan wuta har sai ya nuna sosai.
Shi ke nan sai a ci dadi lafiya.
Ku ma kuna iya jarawaba.