A ranar Jumma’ar da ta gabata ne aka nada Alhaji Umar Kabir Umar II a matsayin sabon Sarkin Katagum da ke Jihar Bauchi. Nadin nasa ya biyo bayan rasuwar mahaifinsa Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Kabiru Umar da kuma zabansa da masu zaben sarki suka yi, da kuma mika masa takardar shaida kan wannan mukami da Gwamnan Jihar Bauchi Muhammadu Abdullahi Abubakar ya yi.
Tun farko, sai da tawagar Gwaman Jihar Bauchi ta gana da hakimai da manyan gari a fadar kafin aka je aka yi Sallar Juma’a, da aka dawo daga Sallah kuma aka nada sabon Sarkin.
Da yake mika takardar shaidar nadin sabon sarkin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Muhammadu Nadada Umar ya yi bayanin cewa masu zaben sarki sun gabatar da sunayen mutum uku ga Gwamnatin Jihar, na farko shi ne Alhaji Umar Kabir Umar, da Birgediya Janaral Yakubu Mu’azu Danlawal din Katagum da kuma Sarkin Dawakin Katagum Alhaji Lele Mukhtar Hakimin Madara. Sannan ya ce gwamnati ta duba wannan al’amari kuma ba ta sauya abin da masu zaben sarki suka yi ba.
Bayan an nada sabon sarkin, sai mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Umar Kabir Umar na biyu ya mayar da jawabi cikin kalamai na kaskantar da kai da godiya ga kowa da kowa, inda ya ce “Babban abin da zan fara, shi ne godewa Allah da Ya kawo mu wannan rana da cikin ikonsa Ya sa na gaji iyaye da kakanni a masarauta da aka kafa a kan musulunci fiye da shekara 200 da suka wuce. Ina godiya ga Gwamnatin Jihar Bauchi, ina godiya wa mutanen Azare da mutanen kasar Katagum, wadanda suka nuna tashin hankalinsu da bakin cikinsu lokacin da mahaifinmu ya rasu, suka cika wajen jana’izarsa a kofar fada, kuma suka rakamu fiye da kilomita goma a kafa. Allah Ya jikansa Ya rahamshehi, Ya sa yana aljannah, Allah kuma Ya kyautata karshenmu”.
Sarki Umar ya ci gaba da cewa “Sakataren Gwamnati ka sanar gwamna cewa mun gode, Allah Ya saka masa da alheri. Ina tabbatar maka da ni da yan’uwana da dukan jama’ar Katagum muna godiya kuma za mu zanto masu biyayya ga gwamnati, da dukan ayyukan gwamnati. Allah Ya kara taimakon gwamna Ya bashi lafiya, Allah Ya kareshi da zuriyarsa baki daya.
“Na yi alkawari ga mutanen Katagum cewa zan yi aiki tsakani da Allah, saboda dukan wanda ya yi sarkin Katagum tun daga ranar da yaje makabartan sarakunan Katagum zai ga yadda shi ma zai zo ya kwanta, ko baka tsoron Allah, idan ka ga inda za ka kwanta, tilas ka yi hidima da jama’a yadda Allah Ya fada. Yan’uwana Hakimai wadanda da muke sarautar hakimci da su, Ku ji tsoron Allah ku rike talakawanku da gaskiya, ku rikesu tsakani da Allah saboda hakkin su ne ayi musu riko da adalci, kuma Allah zai tambayeku, Hakiman da kuka sauke mutane kuka nada wakilai, baya ga Dagaci, amma kuka nada wakilai suna harkar mulki, wannan ba daidai bane, idan Dagacinka baya maka aiki yadda ya kamata, ka rubuto, ka gaya mana idan ba zai gyaru ba sai a saka wani, idan kasan ka kwace musu, ka je ka maida, saboda haka zan bada lokaci musamman a dukan mako ko wata wanda duk talakan da yake da kuka zai zo ya sameni kai tsaye ya fada mini kar kowa ya tareshi.”
Sabon Sarki ya kuma hori talakawa da cewa “Ku kuma Talakawa ku yi biyayya ga hukuma, Allah Ya taimakemu Ya bamu sa’a, Allah Ya sa mu gama lafiya. Iina mika godiyata ta musamman ga kannai da Baffanu wadanda suka janye, suka ce ni in nema wannan sarauta, ba don basa so ba, ba don basu isa ba, sai don zumunci, sai don mu kara hada kanmu.
In sha Allahu ba zan ci amanarku ba, zan rikeku a matsayin iyaye. Godiyata ta Musamman wa masu zaben sarki, ina so jama’a su sani cewa tun da aka fara wannan abu har aka kare ko sisin kwabo bai shiga tsakanina da su ba, Na je wajensu na nemi alfarma amma zance sisin kwabo wallahi babu wanda ya nemi wani abu a wajena, don haka na gode muku. Ina kuma godiya ga sarkin Azare, wanda ya zo da kansa ya sameni ya ce zuriyarsu na Sarkin Azare Mustafa sun bar mana ba za su nema ba, wanda zuriya ce wanda mun yi gwagwarmayan sarauta da su shekara 70 da suka wuce, amma ya zo ya kashe wutar wannan sarauta, ya ce dashi da ‘yan uwansa gaba daya sarki mai rasuwa bai kashe gidansu ba, don haka ba dalilin da za su zo su ci gaba da wannan abu. Ina kumka godiya ga sauran ‘yan uwana, wadanda kuma muka nemi sarautar nan da su, dama haka sarauta ta gada. An riga an gama, ya riga ya wuce, mu dawo mu zama yan’uwa, mu ciyar da kasar Katagum gaba mu hada kan yan’uwanmu, na mika muku hannun zumunci ina fata za ku karba don mu ci gaba da zumunci, Na gode Allah Ya saka muku da alheri”.
Da yake bayyana yadda suka zabi sabon Sarkin, daya daga cikin masu zaben sarki, Galadiman Katagum Alhaji Usman Mahmud ya ce, “Mun nemi mutane na kasa da yawa su ba mu shawara, mun nemi shawarar malamai a wajen masarauta, wadansu jama’a mutanen kirki da dama su ma sun zago sun ba mu shawara, kuma sashe na shawarwarin da suka ba mu mun yi amfani da su, Allah cikin ikonSa da kuma addu’a da aka yi, sai abun ya zo cikin sauki, wannan aiki da Allah Ya dora mana kuma hukuma suka dora mana, nan da nan sai Allah Ya ba mu basira da nasara muka samu sunaye guda uku da za mu aika wa Gwamnatin Jihar Bauchi, Kafin wannan lokaci, da ma lokacin da Allah Ya yi wa Mai martaba wa’adi, mun aika wa gwamnati, ita kuma gwamnati bayan da aka yi sadakar uku, Gwamna ya tafi ya bar sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi ya mana bayanin matakan da za mu bi, a cikin matakan guda hudu, na daya dai ya zamo mai neman sarautar nan sai jinin sarauta, na biyu ya zamo mai kwazo, kuma sai mai liminin sarautar, kuma zai yi biyayya ga hukuma, zai yi biyayya ga doka, wanda kuma ya san shi kansa bai fi karfin doka ba, wadannan ka’idodi guda hudu su aka ba mu mu yi nazari a kansu, mu zabi wadanda za su iya bin wadannan dokoki, kuma suka cika sharuddan da aka shimfida.
A jawabinsa Sarkin Yakin Katagum Alhaji Abubakar Muhammad ya ce ya godewa Allah da Gwamnan JIhar Bauchi da daukacin al’ummar masarautar Katagum, Jihar Bauchi da Najeriya baki daya saboda yadda suka tasusayawa al’ummar masarautar bisa rashin sarki da su ka yi, kuma suka taya mu murnar cewa babban dan sarkin da ya rasu shi ne ya gajeshi, sai ya roki Allah Ya baiwa sabon sarkin zuciya da karfin hali da zai rike jama’a cikin adalci don mahaifinsa bai ki kowa ba. Ya kuma roki Allah Ya tayashi riko Ya albarkaceshi Ya kuma albarkaci dukan wadanda suke da hannu wajen samun nasarar wannan sarauta.
A nasa jawabin, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayalle, Ajiyan Katagum ya ce ba abin da za mu ce sai godiya ga Allah madaukakin sarki mai yin yadda yake so, abubuwan da duk muke so idan ba shi yake so ba, ba za su yiwu ba, saboda haka muna godewa Allah, Allah Ya jikan Sarki Muhammadu Kabiru, kuma Allah Ya taimaki wannan Sarki Umaru Ya zaunar da kasarmu lafiya, muna kuma godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Bauchi, Allah Ya saka masa. Jama’a sun yi farin cikin wannan nadi da aka yi wa sabon sarkin ko ina sai kade kade da bushe bushe Jama’a suna raha suna farin ciki.
Shi dai sabon Sarkin Katagum na sha biyu, Alhaji Umar Kabir Umar na Biyu an haifeshi ne a ranar 25 ga watan Afrailun 1957, ya fara karatun Firamare a 1963- 1969, Makarantar Sakandare da ke garin Azare 1969-1974, Ya halarci Kwalejin share fagen shiga Jami’a a shekarar 1974, sai ya kuma halarci Jamiar Bayero da ke Kano daga 1977 zuwa 1981, inda ya karanci ilimin sanin Tarihi, sannan ya je ya yi aikin yi wa kasa hidima a Jihar Kwara, tsakanin 1981 -1982. Ya fara aikin Gwamnati a Bauchi a 1982, inda ya zama jami’in mulki a ma’aikatu dabam dabam, da suka hada da ilimi, kiwon Lafiya, gidan gwamnati da ma’aikatar yada labarai.
A shekarar 1992 sai ya yi sauyin aiki daga Gwamnatin Jiha ya koma Gwamnatin Tarayya, inda ya rike mukamai dabam dabam har zuwa babban sakatare kafin ya yi ritaya. A fannin harkokin sarauta, an nadashi Hakimin Shira a 1993, sarautar da ya rike har zuwa ranar 15-12- 2017 da aka nadashi Sarkin Katagum na 12.