A zaben da aka gudanar na kananan hukumomi a jihar Gombe a ranar Asabar, Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun ciyamomi 11 da na kansiloli 114, a zaben da aka yi ba tare da an kai akwatunan zabe kowacce mazaba ba.
Mazabu uku ne kawai a kowanne bangaren mazabar Sanata aka kai akwati daya na Gwamna a Gombe ta Arewa da mataimakin sa a Gombe ta Kudu da na shugaban majalisar dokoki a Gombe ta Tsakiya.
- Jonathan na da ’yancin tsayawa takara a zaben 2023 —PDP
- Matsalar tsaro: Secondus ya bukaci Buhari ya yi murabus
Wakilin mu da ya ziyarci garin Luggerewo, inda shugaban majalisar dokokin Abubakar Muhammad Luggerewo, ya jefa kuriar sa cikin dandazon jama’a wanda banda akwatin mazabar sa ba wani akwati da aka fitar a yankin baki daya bayan jefa kur’iar sa kuma aka rufe akwatin.
Jama’a sun fito domin jefa kuri’u a wasu mazabun a jihar amma rashin fitar da kayan zaben yasa suka hakura, suka koma gidajen su.
Dama a ranar Talata da jamiyyar ta APC ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben kananan hukumomin ta fada cewa duk Najeriya jam’iyya mai mulki ce take cin zabe dan haka ba za su bar wata jamiyya tama fito ba domin APC kadai ke takara a jihar.
Wasu jama’a da wakilin mu ya zanta da su a Gombe kan rashin fitar da akwatin zaben sun bayyana cewa sun so su jefa kuri’ar su wanda ko da wanda suka zaba bai musu komai ba suna da damar yin magana amma rashin yin zaben bai musu dadi ba.
Shi ma gwamna Inuwa Yahaya, ya jefa tasa kuriar ne a mazabar sa ta cikin gari a unguwar Jekadafari a sakandaren kimiyya ta gwamnatin jiha tare da wasu magoya bayan sa.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe Saidu Shehu Awak, ne ya sanar da wadanda suka lashe zaben a kananan hukumomi 11.
Wadanda suka sami nasarar sun hada da Usman Abubakar Barambu a Akko, Balanga Garba Umar a karamar hukumar, sai Billiri Magret Bitrus, da Jamilu Ahmed Shabewa a Dukku da Ibrahim Adamu Chalu a Funakaye.
Sauran sune Aliyu Usman Haruna a karamar hukumar Gombe sai Faruk Aliyu Umar a Kaltungo da Ibrahim Buba a Kwami, Musa Abubakar, Nafada sai Yohanna Lahary a Shongom da kuma Shu’aibu Buba Galadima a karamar hukumar Yamaltu-Deba.