An samu tashin hankali da satar akwatunan zabe a wasu rumfuna a zaben Kanana Hukumomin Jihar Ondo da ya gudana ranar Asabar.
Wakilin Aminiya ya ce a wasu rumfunan an samu kwacen takardun jefa kuri’a da kuma cushen kuri’u a zaben da hukumar zaben jihar ta gudanar.
A rumfa ta 19 a Mazaba ta 4 a Karamar Hukumar Akure ta Kudu, masu jefa kuri’a sun koka da cewa wasu mutane da suke zargi ‘yan Jam’iyyar APC ne sun kwace akwatin zaben.
Sun ce wasu mutane sun je rumfar zaben suna ba su N30,000 cewa su zabi APC amma suka ki amsar kudin.
Shugabar Mata ta Jam’iyyar SDP a mazabar, Misis Bisi Aderemi ta ce ‘yan daba a kan babura da suka yi goyon uku-uku dauke da muggan makamai sun kwace akwatin zaben da ragowar takardun dangwala kuri’a suka tafi da su.
Ta ce wani jigo a APC da aka sakaya sunansa ya yi mata tayin N30,000 ta bari su dauke akwatin zaben rumfar.
Dan takarar Kansilan SDP a Gundumar, Joseph Olorunfemi Kehinde, ya zargi ‘yan daba daga APC da bin rumfunan zabe suna cusa takardun jefa kuri’ar da suka riga suka dangwala a cikin akwatunan zabe.
— ‘Zaben ya gudana cikin lumana’
Sai dai a wasu sassan jihar kuma zaben ya gudana cikin lumana.
Gwamna Rotimi Akeredolu ya jefa kuri’arsa a rumfa ta 5 a Gundumar Ijebu Owo a Karamar Hukumar Owo inda komai ya tafi lami lafiya.
Akeredolu ya ce yadda zaben ya gudana babbar nasara ce kuma ya ji dadin fitowar mutane da yawa.
Da yake magana da ‘yan jarida a Idanre, Karamar Hukumar Idanre, Shugaban APC na Jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya ce ba a samu hatsaniya ba a garin.
Adetimehin ya kirayi ‘yan jam’iyyar da su sake yin hakan kuma su yi tuturuwa a lokacin zaben gwaman da ke tafe a watan Oktoba.
Ya yaba wa jami’an hukumar zaben bisa isowar kayan zabe a kan kari da kuma jami’an tsaro da ya ce sun yi aikinsu yadda ya kamata.
Alex Ajipe, Shugaban kamfanin Klick Konnect, bayan jefa kuri’arsa a rumfa ta 16 a Mazabar Emure, Karamar Hukumar Owo, ya ce zaben ya gudana lami lafiya.
Ya ce an kawo kayan zabe a kan kari rumfar, inda wasu mutane suke kan layi tun karfe shida na safe.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Bamidele Oleyelogun, ya ce akwai kwarin gwiwa a yadda mutane suka fito sosai da yadda komai ya gudana lafiya.
Ya bayyana haka ne bayan ya yi zabe a Gundumar Isarun/Erigi da ke Karamar Hukumar Ifedore.
Ya ce hukumar zaben jihar ta kokarta sosai wajen isar da kayan zabe zuwa rumfuna a kan lokaci kuma ba a samu tashin hankali ba.