An zargi wani jami’in ɗan sanda da yi wa wata yarinya mai shekara 17 a duniya fyaɗe a ofishin ’yan sanda na yankin Ogudu da ke Jihar Legas.
Tun da farko jami’in ya yi alƙawarin taimaka wa yarinyar wajen gano wayarta da aka sace, wadda ɓarayi suka sace.
- Shekara 100 a duniya: Sheikh Dahiru Bauchi ya sake kafa tarihi
- An kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya a Ekiti
Ya ji lokacin da yarinyar ke tattaunawa da mahaifiyarta game da sace wayar, sai ya buƙaci ya taimaka musu.
Da isa ofishin ’yan sandan, jami’in ya yaudari yarinyar, inda ya ce akwai kuskure game da lamarin bibiyar wayar.
Daga nan sai ya yaudare ta zuwa ofishinsa, ya kulle kofa, ya yi mata fyaɗe bayan ya yi mata barazana da bindiga.
Jami’in ya kuma yi mata barazanar cewa kullum sai ta je ofishinsa idan aka tashi daga makaranta.
Mahaifiyar yarinyar, Misis Aramide Olupona, ta zargi ‘yan sanda da yunƙurin boye laifin.
Ta bayyana cewa ’yan uwan ɗan sandan su roƙe ta, amma ta dage wajen nema wa ‘yarta adalci, wadda a yanzu ta ke cikin wani hali kuma tana son kashe kanta.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayar da lambobin miƙa ƙorafi ga ’yan sanda amma bai ce komai kan lamarin ba.