Hukumar Babban Birnin Tarayya ta yi rusau a babbar cibiyar hada-hadar ’yan canji da ke unguwar Zone 4 da ke Abuja.
An rusa rumfunan wucin gadi da bacoci tare da sare bishiyoyi a yayin aikin rusau din da aka gudanar ranar Laraba.
Daraktan Sashen Kula da Gine-gine na hukumar, Mukhtar Galadima, wanda ya jagoranci aikin, ya bayyana wa ’yan jarida cewa bata-gari suna amfani bacocin da rumfunan wucin gadin da ke wurin a matsayin maboyarsu a birnin.
Mukhtar Galadima ya kara da cewa wurin ya zama cibiyar masu aikata manyan laifuka, wanda hakan barazana ce don haka ya zama dole a kawar da ita.
A cewarsa, lura da yadda wurin ya zama abin kyamar, matakin da aka dauka zai kara fito da kyawun birnin na Abuja.
Ya kara da cewa, ya zama wajibi ga ’yan canji su rika gudanar da harkokinsu a wuraren da aka ware musu ba a karkashin bishiyoyi ba ko a cikin daji kamar yadda ake yi a Zone 4.
Amma ya ce aikin nasu ba shi da alaka da neman musguna wa ’yan canji, illa kawai neman tabbatar da tsafta da kuma tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a.
Da aka tambaye shi dalilin rashin gina filin da suka yi rusau din, sai ya ce ana shari’a ne a kan filin, ana jira ne kotu ta yanke hukunci.
“Amma duk da haka tsaron rayuka na da muhimmanci, shi ya sa dole muka dauki wannan mataki,” inji shi.