✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi na zama Minista a Gwamnatin Jonathan — Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata David Mark ne ya taimaka masa ya zama Ministan…

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata David Mark ne ya taimaka masa ya zama Ministan Abuja a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da hanyoyin raya yankunan karkara guda uku masu nisan kilomita 35 da za a yi su a kan kudi sama da Naira biliyan bakwai da aka gudanar a Katanga Hedkwatar Karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi.

Ya ce “David Mark ya taimaka min kwarai da gaske a rayuwata shi ya taimaka min na zama Minista kuma shi ne ya roki Shugaban Kasa Jonathan da cewa ya maida ni a mukamin Ministan Abuja a karo na biyu.

“Saboda wannan karimci da ya yi min ina godiya wa Allah kuma David Mark ya amfani rayuwata kwarai da gaske.”

“Ba zan manta ba kuma ban taba fadar haka a wani wuri ba sai yau a nan,” inji gwamnan.

Hanyoyin da aka kaddamar sun hada da hanyar da ta tashi daga Warji zuwa Gwaram cikin Jihar Jigawa mai nisan kilomita 13.5, sai hanyar da ta tashi daga Bogoro zuwa Lusa a Karamar Hukumar Bogoro mai nisan kilomita 11.2 sai kuma hanyar da ta tashi daga garin Boi da ke Karamar Hukumar Bogoro zuwa Tapshin da ke Karamar Hukumar Tafawa Balewa .

Gwamnan ya ce an bude wadannan hanyoyi ne domin a bunkasa tattalin arzikin al’ummar da ke zaune a wadannan yankuna kuma a saukaka musu yanayin rayuwa.

Sai ya jaddada kudurin gwamnatinsa na yin ayyukan alheri a dukkan yankunan kananan hukumomi 20 da ke jihar.

Da yake kaddamar da aikin hanyoyin Sanata David Mark ya ce Gwamnan Bauchi da mataimakinsa mutane ne da suka taimaka masa wajen tsayawa da nuna masa goyon baya lokacin da yake shugabancin Majalisar Dattawa ta Najeriya.

Ya ce “irin goyon bayan da suka nuna masa ya sa ya zamo ba jagora ba ne a kansu ba illa dai shi ma’aikacinsu ne mai yi musu hidima, cikin jagorancin don a gina kasa.”

Ya yaba wa Gwamnan Bauchi saboda wannan babban aiki da ya kawo, ya kuma shawarci masu mulki da su rika tafiya da dukkan al’umma wajen ayyukan ci gaba.