Zainab Usman Aliyu, ko Zainab 3SP kamar yadda wasu ke kiran ta, ita ce ta fito a bidiyon wakokin nan na Sambisa wadanda suka yi fice a kafofin sada zumunta.
Wannan ne ma ya sa ake yi mata lakabi da Zainab Sambisa, ko Amaryar Sambisa.
A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu, ta bayyana yadda ta shiga harkar wakoki da fina-finai da kuma yadda wadannan wakoki suka daukaka ta a duniya.
- Tun Asali Na Yi Makwabtaka Da Sambisa —Yamu Baba
- Yadda Muka Shirya Bidiyon Wakar Sambisa —Darakta Abubakar 3SP
Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarki?
Zainab: Gaskiya ni haifaffiyar Garki – Abuja – ce; a can aka haife ni, har Allah Ya sa na girma na fara wannan harka ta fim, daga nan na koma Kano, daga nan kuma na dawo nan Jos.
Ana kiran ki da Zainab 3SP. Mece ce alakarki da wannan kamfani na 3SP?
To, alakakata da wannan kamfani na 3SP ita ce zaman amana da kuma rike ni da suka yi.
Saboda farkon harkata ta fina-finan Hausa a Abuja na fara daga nan na tafi Kano na ci gaba.
Sai Allah Ya sa wannan kamfani ya kira ni zuwa nan Jos, kuma da na zo irin yadda suka rike ni sai ya sa na ji ina sha’awar zama a kamfanin.
A wannan lokaci ne kika fara shiga wannan harka ta wasan kwaikwayo, kuma mene ne ya ba ki sha’awar shiga?
Na fara wannan sana’a a shekara ta 2018.
Da farko ban taba jin sha’awar wannan harka ta fim ba sai da wani kawuna, wato kanin mahaifiyata – akwai wani fim da za a yi mai suna Tuntube sai ya kira ni ya ce “za mu yi fim, ina sha’awar na sanya ki a ciki”.
Sai na ce a gaskiya ba zan yi fim ba, saboda an ce ’yan fim ’yan iska ne.
Sai ya ce “bari na gaya maki, kowace irin sana’a ce kake yi, za ta iya kai ka wuta, kuma za ta iya kai ka Aljannah.
“Ya danganta ne da yanayin yadda ka shiga wannan sana’a: idan kin shiga da mutunci, har ki kare za ki kasance da mutuncinki”.
A haka ma ban yarda zan yi ba sai da muka je wajen daukar fim din; muka yi wajen kwana 10 muna zuwa har na saba da mutane.
Daga nan na fara sha’awar shiga wannan sana’a; kuma na fara shiga wannan harka ne a Abuja.
Ban da bidiyon Sambisa, kina fitowa a bidiyon wasu wakoki ne?
Sosai kuwa, ina fitowa a bidiyon wasu wakoki da dama.
Domin na fito a bidiyon wakar “Jinin Jikina” da “Sabuwar Duniya” da bidiyon wakoki da dama.
Kuma duk wannan kamfani na 3SP ne ya shirya.
Me za ki ce a kan wakokin Sambisa, kuma a ciki wacce ce ta fi burge ki?
Gaskiya babu abin da zan ce kan wakokin Sambisa, sai dai na yi godiya ga Allah, saboda ta dalilin wadannan wakoki aka gan ni aka san ni.
Gaskiya fitowar bidiyon wadannan wakoki ta sa na kara daraja a idon mutane kuma na kara samun masoya, domin zai yi wuya na je wani waje a ce ba a gane ni ba.
Wani lokacin ina cikin tafiya sai na ji an kwala mini kira ana cewa “Zainab Sambisa”.
Ina alfahari da wannan al’amari.
[Ni] ce nake cewa [a yi wakokikin Sambisa]; kuma ni ce nake sayo wakkokin, kuma ni ce nake daukar nauyin [shirya bidiyon].
Kuma a cikin wakokin Sambisa, gaskiya na fi son wakar Sambisa ta biyu.
Abin da ya sa na fi son wakar kuma shi ne a lokacin da muka yi bidiyon wakar Sambisa ta farko ina matukar son ta, amma da wakar Sambisa ta biyu ta fito, sai na ji na fi son ta.
Wacce rawa ce kika taka wajen sayen wadannan wakoki na Sambisa daga wajen wanda yake rubuta su?
Wakar Sambisa ta farko na jita ne, bayan ya riga ya yi na saye ta.
Ta biyu kuma zuwa ta uku, ni ce nake cewa ya yi. Kuma ni ce nake sayo wakar, kuma ni ce nake daukar nauyin wakar.
Kudaden da ake kashewa, tun daga farkon shirya bidiyon wakar, har zuwa karshe ni ce nake daukar nauyi.
Shi kuma mai ba da umarni ya yi nasa aikin, don haka zan ce wannan waka tawa ce da kamfanin 3SP.
Me za ki ce a kan barazanar da Sani Liyaliya ya yi cewa ba zai kara ba ku wakarsa ba, saboda ba kwa sanya sunansa a bidiyon wakar?
Gaskiya ni ban ji wannan magana ba.
Kuma ni tsakanina da Sani Liyaliya har yanzu muna mutunci da juna, ko yau na kira shi a waya zai daga mu yi magana.
Kuma maganar ba mu sanya sunansa a wakar Sambisa ta biyu da ta uku – a ta farko mun sanya sunansa, a waka ta biyu mun sanya sunansa a wakar, a ta uku ma mun sanya sunansa a wakar.
Amma da yake na yi masa alkawarin za mu sanya sunansa, Allah ya mantar da mu ba mu sanya ba.
Amma wallahi bayan wannan, ni ban san wani abu na fada tsakaninmu da shi ba, ko kuma ya ce ya daina ba mu wakokinsa ba
A matsayina na wadda ni ce nake zuwa wajensa na karbo wadannan wakoki ni ba mu yi wannan magana da shi ba.
Don haka ni a wurina babu wata matsala a tsakaninmu, domin a yanzu ma, akwai sababbin wakokinsa da muka yi, kamar “Matar Sarki” da “A Wanki Gara” kuma akwai wasu da dama da ba mu gama aikinsu ba. Kuma duk kwanan nan muka karbo su daga wajensa.
Mec ce dangantakarku da wanda kuke fitowa a bidiyon wannan waka, wato Yamu Baba, shin saurayinki ne ko yaya abin yake?
Yamu Baba ba saurayina ba ne, maigidana ne a wannan kamfani na 3SP.
Kina fitowa a waka ne kadai, ko har a fim ma kina fitowa?
Ina fitowa a fim domin na fito a fina-finai da dama. Na fito a fim din “Juyin Yanayi” da “Ranar Rabuwa” da “Tuntube” da “Zalihat” da “Babban Gaushi” da “’Ya’yan Baba”.
Me ya sa kika bar fim, kika dawo waka?
Ban bar yin fim ba, domin har yanzu ina fitowa a fim.
Ko gobe aka kira ni na zo na yi fim, zan zo na yi.
Kuma ina ci gaba da yin wakokin kuma ina yin fim din barkwanci, babu abin da ba na yi a wannan harka.
Da fim da waka wanne ya fi burge ki?
Gaskiya a da fim ya fi burge ni, amma yanzu na fi son yin waka saboda waka aba ce mai sauki wajen tura sako.
Domin za ka ga wani fim kafin a fitar da shi za a dauki tsawon kamar watanni biyar.
Amma waka za ka iya yin ta, a cikin mako daya zuwa biyu, ka sake ta ta je wajen da ba ka yi tsammani ba.
Saboda haka na fi son waka a kan fim.
Ganin irin yadda yanzu mutane suka fi mayar da hankali a kan waka yaya kike ganin barazanar da take yi ga harkar fim?
Gaskiya waka ba za ta zama barazana ga harkar fim ba, domin da waka da fim duk abu daya ne.
Wadanne irin nasarori ne kika samu a wannan harka?
Gaskiya na samu nasarori da dama domin na karbi lambobin karramawa kamar na fim din “Zalihat” da wakar “Sambisa”.
Kuma na samu cigaba sosai a wannan harka, don haka babu abin da zan ce wa wannan harka, sai dai na yi godiya ga Allah.
To, mene ne sakonki ga abokan sana’arki, da ’yan kallo baki daya?
Abokan sana’armu, zan ce mu kara jajircewa; idan muka kara jajircewa, za mu kai inda ba mu zata ba.
Su kuma ’yan kallo da masoyanmu, muna mika masu godiyarmu saboda su ne suke karfafa mana gwiwa a kan abubuwan da muke yi.