✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi Maulidin Shehu Tijjani a Katsina

A ranar Asabar da ta gabata ce aka yi bikin Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani a garin Katsina inda Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari da…

A ranar Asabar da ta gabata ce aka yi bikin Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani a garin Katsina inda Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari da Sheikh Dahiru Bauchi da sauransu suka halarta.

A jawabin Gwamna Masari ya nuna farin cikinsa kan yadda mabiya da shugabannin Darikar Tijjaniyya suke ta yi wa bangarorin gwamnati addu’o’in samun zaman lafiya tare da kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a halin yanzu a kasa baki daya.

Gwamna Masari ya ce gwamnati za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga harkokin mabiyan saboda irin yadda suke yi wa gwamnatin APC biyayya tun daga shekarar 2015.

A jawabin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yaba wa Gwamna Masari kan amincewa da bayar da filin da aka gudanar da Mauludin da kuma tallafin kudi don ganin cewa an yi taron kamar yadda ya kamata.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, akwai jikokin Shehu Ahmadu Tijjani da na Sheikh Ibrahim Kaulaha da suka halarci wannan Mauludi. Malamin ya tabbatar da cewa za su ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya tare da kawo karshen matsalar tsaro da suka addabi kasar nan.

Tun farko a jawabin maraba, Shugaban Kwamitin Shirye-Shiryen Mauludin Sheikh Hadi Sheikh Ja’afaru ya nuna matukar godiyarsu ga Gwamna Masari kan yadda yake nuna kula kan harkokin da suka shafi addini musamman a bangarensu na Tijjaniyya.

Bayan jawabai daban-daban da aka yi kan dalilai tare da muhimmancin wannan biki na Mauludin Shehu Ahmadu Tijjani, an kuma yi karatu Alkur’ani Mai girma.

Maulidin ya gudana ne a filin wasa na tunawa da Muhammadu Dikko da ke cikin garin Katsina.