An yi jana’izar fitaccen shugaban Fulani, dan kishin kasa kuma tsohon dan jarida, Alhaji Sale Bayeri.
Sheikh Muhammad Nasir Abdulmuhyi ne ya jagoranci Sallar Jana’izar Alhaji Sale Bayari tare da binne shi da safiyar ranar Juma’a, kamar yadda addnin Musulunci ya tanadar.
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 – Gwamnan Bauchi
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
- CBN na mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudade – ACF
- Ya kamata a hana makiyayan kasashen waje shigowa Najeriya kiwo – Ganduje
Sale Bayeri ya rasu ne a ranar Alhamis da dare a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shugaban GAFDAN reshen Jihar Filato, Garba Abdullahi Muhammad ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar Bayeri.
Kafin rasuwarsa, Bayari ya kasance Shugaban Kungiyar Gan Allah Fulani (GAFDAN), sannan tsohon Sakataren Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), inda ya yi aiki na kimanin shekara 20.
Sannan ya halarci taruka da dama na ciyar da kasa da talakawa gaba, kazalika, ya kasance mai taimakon rayuwar mutane.