✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aka Yi Jana’izar Jagoran Tijjaniyyan Gombe, Muhammad Habib

An gudanar Jana'izar Jagoran Darikar Tijjanan Jihar Gombe, Khalifa Muhammad Habib.

An gudanar da jana’izar Jagoran Darikar Tijjana na Jihar Gombe, Khalifa Muhammad Habib.

Ya rasu ne wata biyu da zamansa jagoran Tijjaniyyan jihar bayan rasuwar Shiekh Muhammad Kobuwa.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar Khalifa Muhammad Habib a matsayin babban rashi ba ga Tijjanawan kadai ba, hat ga illahirin Musulmin Jihar.

Inuwa ya ce rasuwar Khalifa Muhammad Habib, ta bar babban gibi a tsakanin Mabiya Darikar Tijjaniya.

A wata sanarwar da Babban Daraktan Yada labarai na gidan Gwamnati Isma’ila Uba Misilli ya fitar ya ce gwamnan ya kadu matuka inda ya yi jimamin rasuwar sa tare da ya yi masa addu’ar Allah jikan sa.

Sannan ya mika ta’aziyyarsa ga ɗaukacin mabiya Darikar Tijjaniya na  Jihar Gombe da ma al’ummar Musulmi baki daya.