An yi Sallar Jana’izar Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu tare da binne gawarsa a Zariya a ranar Asabar 2 ga watan Janairu, 2021.
Da misalin karfe 10 na safe ne dubun dubatar mutane suka halarci sallar jana’iza Iyan Zazzau wanda ya rasa a daren Juma’a sakamakon rashin lafiya a Legas.
- Rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau ta girgiza Buhari
- Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga —Mai jego
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
Safiyar Asabar din ce aka kawo gawarsa Zariya daga Legas. A baya iyalan mamacin sun shaida wa Aminiya cewa za a yi jana’iyar bayan Sallar La’asar a ranar Juma’a amma hakan bai samu ba.
Sallar Jana’izar da aka gudanar a Babban Masallaci Juma’a da ke Tsohuwar Kwata ta gudana ne karkashin jagorancin Babban Limamin Masarautar Zazzau, Liman Dalhatu Kasimu, a Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.
Bayan sallar ce kuma aka rufe mamacin wanda ya bar duniya yana da shekara 70 a gidansa da ke GRA Sabon Gari.
Saboda taron jama’a ba za a iya tantance iya muhimman mutanen da suka halarci jana’izar ba sai dai kusan duk masu rike da mukamai daga Massrautar Zazzau sun samu halartar jana’izar.