✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi artabu tsakanin APC da PDP a Edo

An yi harbe-harben tare da farfasa motoci da kuma jikkatar mutane

Magoya bayan jam’iyyun APC da PDP sun yi artabu a fadar Oba Ewuare II na Benin, a Jihar Edo, inda da yawa daga cikinsu suka jikkata.

Ana zargin rikicin ya barke ne tsakanin magoya bayan dan takarar gwamnan APC Osagie Ize-iyamu da na PDP, kuma Gwamna Jihar mai ci, Godwin Obaseki.

Wata majiya ta ce an yi harbe-harben bindiga a wurin rikicin, al’amarin da ya haifar da farfasa motoci da jikkatar mutane.

Rikicin ya soma ne a jiya lokacin da Gwamna Obaseki da wasu gwamnonin PDP suka kai ziyara a fadar basaraken kafin kaddamar da bukin neman zaben sa karo na biyu a matsayin gwamnan Jihar.

Majiyar ta ce, ‘yan PDP sun shigo fadar suna wakar dan takararsu sai magoya bayan APC suka rika rera tasu wakar, wanda hakan ya tayar da fitinar.

Rahotanni sun ce jim kadan bayan Gwamna Obaseki ya bar gidan Oba ne fada ya kaure, har magoya bayansa suka gayyato mutanesu daga filin taron saboda an fi su yawa.

An ce zuwan ‘yan sanda ya kwantar da rikicin da aka dauki lokaci ana yi.

Da yake magana kan rikicin, Obaseki ya yi kira ga mutanensa da su rika tausar zuciyarsu kuma su guji ramuwa.

Kokarin da wakilinmu ya yi na samun karin bayani daga kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Chidi Nwanbuzor, ta wayarsa ya ci tura.