Dakarun rundunar ’yan sandan Najeriya sun tarwatsa daruruwan ’yan kungiyar Shi’a wadanda suka yi shirin yin tattaki daga Kano zuwa Zariya.
Wani ganau mai suna Malam Abdulrahman Bukar ya ce membobin kungiyar Shi’a sun taru a daidai shataletalen kamfanin Dangi kusa da sakatariyar Audu Bako yayin da rundunar ’yan sandan ta jibge dakarunta a wurin.
Ya ce ’yan sanda sun rika harba barkonon tsohuwa tare da harbin bindiga a sama yayin da ’yan shi’ar suka fara tattakin zuwa hanyar Zariya.
Wani ganau ya ce yayin da ’yan Shi’ar suka fara jifan ’yan sanda da duwatsu sai ’yan sandan suka fara harba barkonon tsohuwa tare da harbi a iska.