✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka tsamo gawar wani matashi a kududdufi

Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta ce tana ci gaba da bincike a kan musabbabin mutuwar wani matashi da ya nutse a cikin wani kududdufi.…

Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta ce tana ci gaba da bincike a kan musabbabin mutuwar wani matashi da ya nutse a cikin wani kududdufi.

Rahotanni dai sun ce matashin mai suna Yusuf Abdullahi dan kimanin shekaru 22 ya nutse ne a wani kududdufi dake garin Danhassan na karamar hukumar Kura ta jihar Kano kuma daga bisani jami’an hukumar suka yi nasarar tsamo gawarsa ranar Lahadi.

Kakakin hukumar, Malam Sa’idu Muhammad ya shaidawa Aminiya cewar ya zuwa yanzu ba su kai ga gano musabbabin rasuwar matashin ba.

“Muna ci gaba da bincike kasancewar yau (Litinin) aka dawo aiki”, in ji Malam Sa’aidu.

Ya kara da cewa, “Mun samu rahoto daga wani mai suna Malam Sadi Ibrahim da misalin karfe 03:42 na yamma [ranar Lahadi] cewar gawar Yusuf na can na yawo a kududdufin.

“Da jin haka ne muka garzaya inda jami’anmu suka yi nasarar tsamo gawar suka kuma danka ta ga Dagacin Garin Kaya, Alhaji Aminu.”

Sai dai ya ce ba su iya tantance ko a ranar da suka samu rahoton rasuwar lamarin ya faru ko kuma ya mutu tun kafin sannan ba.