Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa an sace miliyoyin kudi a gidan gwamnatin jihar.
Daya daga cikin hadiman gwamnan kan harkokin yada labarai, Al-Amin Isa ne, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.
- Masar Ta Gargadi Habasha Kan Tsagewar Dam da Suke Takaddama
- An gurfanar da basarake a kotu kan dabanci a fada
Isah, wanda bai bayyana adadin kudaden da aka sace ba, ya ce tuni ‘yan sanda suka yi wa wasu daga cikin wadanda ake zargi tambayoyi.
Rahotanni sun bayyana cewar wadanda ake zargin sun yi awon gaba da Naira miliyan 31 daga ofishin mai kula da harkokin kudi na gidan gwamnatin jihar.
An kuma tattaro cewa wannan shi ne karo na biyu a wannan shekara da ake sace kudi a gidan gwamnatin jihar.
A watan Janairun 2020, an yi wa ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa sata, inda aka sace Naira miliyan 16.
Kazalika, a watan Yulin 2022, wasu ‘yan bindiga sun harbe Aminu Darma, mai karbar kudi a ofishin sakataren fadar gwamnatin jihar tare da yin fashin Naira miliyan 61 a babban birnin jihar.