’Yan bindiga sun kashe yara uku suka yi garkuwa ’yan uwansu suka kuma yi garkuwa da iyayensu mata a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Maharan sun bude wa motar mamatan da ke hanyarsu ta zuwa Kaduna wuta ne a unguwar Dagedda daura da garin Buruku a safiyar Alhamis.
- Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko
- Ganduje ya yi rusau a ‘filin Sheikh Abduljabbar’
Wani tsohon ma’aikacin Hukumar Kula da Gidajen Yaro, Muhammadu Gagare ya ce ’ya’yansa da matansa na daga cikin wadanda ’yan bindigar suka kashe da wadanda aka yi garkuwa da su.
“An kashe ’ya’yana uku, Saidu, Abdulrashid da Rahmatu, aka yi garkwa da uku tare da matana biyu a ranar.
“Har yanzu wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntube mu ba. Babu waya a tare da matan nawa a lokacin da abin ya faru,” inji shi.
Ya ce daya daga cikin ’ya’yan nasa da aka kashe dalibi ne da ke karatu a Kaduna.
Rahoton da Aminiya ta samu ya nuna motar ta kwace wa direban ne bayan ’yan bindigar sun harbe shi.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sn bude wa matafiyan wuta ne a lokacin da ’yan bindigar ke tsere wa jami’an tsaro da ke sintiri.
Aruwan ya tabbatar da mutuwar mutum shida a nan take da suka hada da Abdurrashid Ya’u, Sa’idu Ya’u, Ramatu Ya’u, Suwaiba Ali, Sulaiman Ustaz da wani karamin yaro.
Kwamishinan ya ce bayan motar ta tsaya, ’yan bindigar sun tafi sun yi tafiyarsu suka bar sauran matafiyan da suka ji rauni.
Fasinojin da suka jikkata sun hada da Ubale Yahuza, Rabiu Ibrahim, Umar Musa, Saude Yusuf, Mohammed Aminu da Kadima Mercy.
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana damuwa game da abin da ya faru, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar samun sauki ga wadanda suka ji rauni.