✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace magidanci a hanyar zuwa filin jirgi a Abuja

Magidancin matarsa suna hanyarsu ta komawa gida daga cikin kwaryar birnin Abuja ne ’yan bindiga suka tare su

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani magidanci a kan hanyar zuwa filin jirgin saman da ke Babban Birnin Tarayya.

Abdullahi Sabo da matarsa suna hanyarsu ta komawa gida daga cikin kwaryar birnin Abuja ne ’yan bindiga suka tare su a Sabon-Lugbe, kan titin zuwa filin jirgin.

Maharan da ke cikin wata mota kirar Golf sun harbe tayoyin motarsa ne suka tilasta masa tsayawa, sannan suka tafi da shi a ranar Juma’a da dare.

Wani makwabcinsa, Mista Daramola Joseph, ya shaida wa rediyon tarayya cewa matar magidancin ta samu ta tsere kafin maharan su kai gare su.

“Harbe tayoyin motarsa suka ne suka yi, suka tilasta wa motar tsayawa, amma kafin su zo wurin motar, matar Abdullahi ta tsere. Amma sun tafi da mijinta,” inji shi.

Da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce za ta bincika kafin fitar da wata sanarwa.

An sace magidancin ne kasa sa da sa’o’i 48 da ’yan bindiga suka kai hari tare da sace mutane a rukunin gidajen sojoji da ke unugwar Kurudu a Abuja.