✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 Yadda aka sace Dala 50,000 a Hedikwatar APC a Abuja

Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa na tattauna batun sace kudin a harabar sakatarriyar jam'iyar

An sace tsabar kudi kudi Dala 50,000, kimanin Naira miliyan 20, a bainar jama’a, a Hedikwatar Jam’iyyar APC da ke Abuja ranar Laraba.

Dalolin, wadanda mallakin wani jami’in APC na shiyyar Kudu maso-Gabas ne, an yi awon gaba da su ne rana tsaka a ayin da yake shiga harabar ofishin, inda ake sayar da fom din takarar zaben 2023.

Bayanan tsaro sun nuna wanda wanda aka yi wa satar, Jami’in APC ne daga Jihar Inugu, kuma bayan da ya shiga Sakatariyar jam’iyyar ne daga bisani aka ga ya fito yana ihun an sace mishi kudi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan jam’iyyar sun yi dafifi a harabar ofishin bayan da aka fara sayar da takardun takarar zaben 2023.

An ce mai kudin ya shiga harabar ofishin ne rike da wayoyinsa guda biyu da kuma kudi a cikin ambulan, inda a karshe aka sace ambulan din kudin aka bar shi da wayoyi.

Lamarin ya sanya wasu ganin laifinsa kan abin da ya faru na kin shiga cikin harabar ofishin da motarsa, yayin da wasu kuma suka dora laifin a kan jami’an tsaro na kin yin aikinsu yadda ya kamata.

A cewar wata majiya, “Sai ji aka yi ya dawo yana ta ihu; Wannan shi ne karon farko da na ga irin haka ya faru a nan. Dandazon ya yi yawa, kila haka ne ma ya sa bai samu shiga da motarsa ba.”

Wata majiya ta daban ta ce, “Da farko ban yarda hakan ta faru ba, sai da na ji ana tattauna batun a wajen taron Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).”

Ya zuwa hada wannan rahoto, Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Barista Felix Morka, ba ya kusa balle a ji ta bakinsa.