✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe ango da abokansa 7 a Adamawa

Wadansu mutane a kauyen Borong da ke Karamar Hukumar Demsa a Jihar Adamawa, sun hallaka wani ango da ke shirin aure a garinsu tare da…

Wadansu mutane a kauyen Borong da ke Karamar Hukumar Demsa a Jihar Adamawa, sun hallaka wani ango da ke shirin aure a garinsu tare da abokansa bakwai, sa’annan suka jefa gawarwakinsu a cikin kogi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa manema labarai cewa, rundunar ta kama wadansu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a cikin ta’asar.

Ya ce wadanda aka kashen, mafarauta ne da suka fito daga kauyen Shani, kuma sun shigo kauyen Borong ne da zimmar ganawa da iyayen amaryar da za a aurar, kwatsam sai jama’ar kauyen suka ankarar da sauran jama’a cewa, sun shigo ne da niyyar kaddamar da farmaki a kan kauyen nasu.

Kakakin ya ce, wadansu mazauna kauyen ne suka shaida wa ’yan sanda lamarin; wadanda daga bisani suka dauke gawawwakin zuwa ofishinsu. Kuma jama’ar kauyen ne suka taru, inda suka kashe angon da abokansa, sa’annan suka jefa su a cikin kogi.

“Angon, wanda dan farauta ne, ya samu rakiyar abokansa ne, dukkansu sanye da kayan farauta kuma rike da bindigogi; al’amarin ya faru ne duk da sun aike da dayansu ya shaida wa takwarorin aikinsu a kauyen Borong, cewa suna shirin shiga garin don ganawa da iyayen amaryar,” inji Kakakin.

Aminiya ta fahimci cewa, angon mai suna, Luka Yakubu, ya je kauyen tare da rakiyar abokansa tara; amma sai suka gamu da fushin jama’ar kauyen-wanda suka kashe su nan take.

Daya daga cikinsu da ya tsira, mai suna Hassan Danladi ya ce, ya kubuta ne daga fushin makasan, saboda ya shiga kauyen ne ba tare da kayan farautar a jikinsa ba.

Sa’annan ya yi kira ga gwamnatin jihar ta tallafa wa iyalan wadanda lamarin ya rusta da su.