Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta gabatar da wasu mutane da aka kama da bindigogi 73 da suke wa ’yan bindiga fasakwauri.
Kwamturolan Zone B na NCS, Bashir Hamisu, ya ce dubun mutanen ukun ta cika ne a lokacin da suke dakon manyan bindigogin 73 da harsasai guda 846 zuwa ga ’yan ta’adda a jihohin Zamfara da Kaduna.
“An kama mutum ukun ne baya mun samu bayanan sirri game da wata mota makare da dogayen bindigogi 73 da harsasai 846 da aka boye a cikin manyan buhunan shinkafa ’yar gida”, inji shi.
Bashir ya ce mutanen sun shiga hannu ne a yankin Zamare da ke Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi.
Ya ce mutanen na taimaka wa hukumar da muhimman bayanai, yayin da take ci gaba da bincike game da inda suke sayo makaman.
Ya kuma yaba wa sauran hukumomin tsaro bisa taimakon da suka bayar wurin damke wadanda ake zargin.