An kama wata motar alfarma kirar Range Rover makare da kusan kulli 300 na tabar wiwi a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Asirin motar da ta dauko tabar wiwin da nauyinta ya kai kusan kilogram 223 ya tonu ne a wurin sintitrin Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA)a kan hanyar.
A yayin bincike ne jami’an hukumar suka gano kusan kowanne sashe na jikin motar, har cikin ‘injinta shake yake da tabar wiwin.
A tattaunawarsa da Aminiya yayin zantawa da ‘yan jarida a wani bangare na bikin zagayowar Ranar Yaki da Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Duniya a hedikwatar hukumar da ke Kano, wanda ake zargin ya ce bai taba zaton jami’an NDLEA za su iya bankado shirin nasa ba.
“Na jima ina wannan harkar, ina kokarin in shigo da kayan ne zuwa Kano ne rana ta baci aka kama ni a hanyar Zariya”, inji shi.
- NDLEA ta kama masu safarar kwayoyi 15 a Kaduna
- NDLEA ta kama wani da ya hadiye kullin kwayoyi 80 tare da wasu 64
Ya ce, “Na dade ina amfani da wannan dabarar kafin azal ta zo min. Na yi nadama matuka kuma ina fatan wannan ya zama na karshe”.
‘Mun kama ton bakwai na miyagun kwayoyi’
Da yake jawabi tun da farko, Kwamandan Hukumar Reshen Jihar Kano, Dr Abdul Ibrahim ya ce, daga lokacin da aka saka dokar kulle zuwa yanzu kadai, hukumar ta kama sama da Ton bakwai na miyagun kwayoyi daban-daban.
“Ko da yake annobar coronavirus ta yi matukar tasiri kan ayyukan hukumarmu, mun sami nasarar kwace akalla Ton daya da digo shida na miyagun kwayoyi daban-daban”, inji shi.
A cewarsa hukumar ta kuma kama kwayar arizona da nauyinta ya kai kusan kilogram 9. Ta kuma kama wata mota makare da tabar wiwi da nauyinta ya kai kusan kilogram 283 a Wudil yayin da ake kokarin shigar da ita jihar Bauchi.
Sai kuma Giram 100 na hodar ibilis da aka kama a hannun wasu masu safarar miyagun kwayoyi mace da namiji.
Kwamandan ya kuma ce yawan sabbin hanyoyin da masu laifin ke bullo da su ya tilasta wa hukumar sauya salon yaki da su.
Ibrahim ya kuma ce hukumar ta sami nasarar gurfanar da mutum kusan 85, kuma 76 daga cikinsu ke zaman jiran shari’a.